Gobara Ta Tashi a Ofishin Gidan Rediyon Najeriya, An Gano Abin da Ya Faru
- Wata gobara ta tashi da harabar ofishin gidan rediyon Najeriya da ke a jihar Legas a tsakiyar makon nan
- Gobarar da ta tashi da yammacin ranar Laraba, 27 ga watan Nuwamban 2024 ta shafi sashen watsa labarai na ginin
- Hukumomin ba da agajin gaggawa sun garzaya zuwa wajen yayin da suka ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar wacce ba a san musabɓabin tashin ta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - An samu tashin gobara a harabar ofishin gidan Rediyon Najeriya da ke Legas.
Gobarar dai ta tashi ne a ranar Laraba a harabar ofishin da ke Lamba 35, kan titin Ikoyi a Legas, lamarin da ya haifar da fargaba.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa ba a san musabbabin tashin gobarar ba yayin da hukumomi suka ƙaddamar da bincike kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumomi sun tabbatar da tashin gobarar
Daraktar hukumar kashe gobara ta jihar Legas, Margaret Adeseye, ta bayyana cewa hukumar ta samu kiran waya da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
Ma’aikatan kashe gobara na Dolphin, Ebute Elefun, da kuma Oba Onitolo sun yi gaggawar ɗaukar matakan shawo kan wutar da ta mamaye sashen watsa labarai na ginin.
"Ana ci gaba da ƙoƙarin shawo kan gobarar da kuma tantance girman ɓarnar da ta yi."
"Ana ba da tabbaci ga jama'a cewa, ƙoƙarin haɗin gwiwa tsakanin hukumar kashe gobara da sauran masu bayar da agajin gaggawa, ciki har da ƴan sanda, ya shawo kan lamarin."
"An yi nasarar tsayar da wutar a ɗakin watsa labarai na ginin. Yayin da har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, kuma ba a samu asarar rayuka ba, ana ci gaba da ƙoƙarin kashe ta."
- Margaret Adeyeye
Gobara ta tashi a hedkwatar ƴan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a hedkwatar rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar Sokoto.
Gobarar wacce ba a iya tantance musabbabinta ba, a safiyar ranar Asabar, 14 ga watan Satumban 2024 ta ƙone ofisoshi a hedikwatar rundunar ƴan sandan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng