Gwamna Buni Ya Rabawa Waɗanda Ambaliya Ta Shafa da Talakawa Naira Biliyan 2.9
- Gwamnan jihar Yobe ya bai wa waɗanda ambaliya ta shafa da talakawa tallafin tsabar kudi Naira biliyan 2.9
- Mai Mala Buni ya kuma rabawa masu kananan sana'o'i 15,000 tallafin Naira biliyan 1.5, inda aka ba kowane ɗaya N100,000
- Ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali wajen inganta fannin ilimi, kiwon lafiya da sauran ɓangarorin da talakawa za su amfana
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yobe - Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ya damƙa tsabar kudi N2,936,000,000.00 ga mutane 25,500 wadanda ambaliyar ruwa ta shafa da kuma marasa galihu a jihar.
Gwamnan ya miƙa waɗannnan kuɗaɗe ga waɗanda ibtila'in ambaliya ya rutsa da su a gidan gwamnatinsa da ke Damaturu, babban birnin Yobe.
Gwamna Buni ya tallafawa masu sana'o'i
Mai Mala Buni ya kuma tallafawa mutane 15,000 masu kananan sana'o'i kowane N100,000 domin su faɗaɗa kasuwancinsu, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake jawabi, gwamnan ya ce wannan wani ɓangare ne na ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi don taimakawa masu karamin karfi da marasa galihu.
Yadda gwamnan ya rabawa mutane tallafi
"Yau rana ce ta farin ciki da muka kaddamar da shiri guda biyu, na farko tallafawa waɗanda ambaliya ta shafa da masu karamin karfi su 25,500.
"Za a bai wa kowane ɗaya daga cikinsu tallafin N50,000 domin su sake gina rayuwarsu ta yadda za su dogara da kansu."
"Domin farfaɗo da ƙananan sana'o'i, za mu rabawa ƙananan ƴan kasuwa 15,000 tallafin Naira biliyan 1.5, kowane zai samu N100,000 domin su bunƙasa sana'o'insu."
- Mai Mala Buni.
Buni ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da bada ilimi kyauta, kiwon lafiya da faɗaɗa hanyoyin fasaha domin inganta rayuwar talaka, Business Day ta kawo.
Gwamna Buni ya amince da sabon albashi
Kuna da labarin gwamnan jihar Yobe ga amince da sabon mafi ƙarancin albashin da za a riƙa biyan ma'aikatan gwamnati.
Mai Mala Buni ya amince da mafi ƙarancin albashi na N70,000 wanda za a fara biyan ma'aikatan gwamnatin jihar daga watan Disamban 2024.
Asali: Legit.ng