Kotu Ta Kori Karar da Aka Nemi Hana EFCC Kama Gwamna idan Ya Bar Mulki a 2027

Kotu Ta Kori Karar da Aka Nemi Hana EFCC Kama Gwamna idan Ya Bar Mulki a 2027

  • Babbar kotun tarayya ta kori ƙarar da ake nemi haramtawa EFCC kama gwamnan jihar Legas bayan ya bar mulki a 2027
  • Mai shari'a Joyce Abdulmalik ta yi fatali da ƙarar bayan lauyan da ke wakiltar Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya bukaci dakatar da shari'ar
  • Tun farko wani lauya mai suna, Darlington Ozurumba ne ya shigar da karar amma gwamnatin Legas ta ce babu hannun mai girma gwamna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ta yi watsi da ƙarar da aka nemi hana hukumar EFCC kama Gwamna Babajide Sanwo-Olu bayan ya bar mulki.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ce ta yi fatali da karar bayan Gbenga Akande, lauyan da ya wakilci Gwamna Sanwo-Olu, ya gabatar da bukatar a dakatar da karar.

Gwamna Babajide Sanwo-Olu.
Kotun tarayya ta kori karar da aka nemi hana EFCC kama gwamnan jihar Legas Hoto: Babajide Sanwo-Olu
Asali: Facebook

Yadda aka nemi hana kama gwamnan Legas

Kara karanta wannan

Abba ya roki Sanusi II da sauran sarakunan Kano alfarma a kan tsare tsarensa

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa a watan Oktoba da ya gabata aka shigar da karar a madadin Gwamna Babajide Sanwo-Olu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani lauya Darlington Ozurumba, ne ya shigar da karar a madadin gwamnan Legas, wanda zai kammala wa’adinsa na shekaru takwas a ranar 29 ga Mayu, 2027.

Lauyan ya shigar da ƙarar hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziki zagon ƙasa watau EFCC kan zargin tana shirin cafke gwamnan da gurfanar da shi bayan ya bar mulki.

EFCC na shirin kama gwamnan Legas

Lauyan ya kara da cewa shirin kama Sanwo-Olu ya sabawa kundin tsarin mulkin kasa kuma ya saba wa hakkinsa na yancin kai da walwala.

Bisa haka ya roƙi kotu ta haramtawa EFCC musgunawa, tsoratarwa, kamawa, tsarewa, yin tambayoyi, ko kuma gurfanar da Sanwo-Olu kan abin da ya shafi mulkinsa a Legas.

Gwamnatin Legas ta musanta shigar da ƙara

Sai dai da take maida martani kan karar, gwamnatin Legas ta ce Sanwo-Olu bai umurci kowa ya shigar da karar EFCC ba.

Kara karanta wannan

Zargin almundahana: Bayan EFCC ta dafe shi, kotu ta yarda a tsare Yahaya Bello

Antoni Janar na Legas, Lawal Pedro, SAN, ya ce za su binciki yadda aka shigar da ƙarar ba tare da sanin mai girma gwamna ba.

Takardar zaman sauraron shari'ar a ranar 31 ga watan Oktoba ta nuna cewa lauyan da wakiltar Gwamna Sanwo-Olu ne kaɗai ya halarci zaman da kotu ta kori ƙarar.

Gwamna Babajide ya dakatar da hadiminsa

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan jihar Lagos, Babajide Sanwo-Olu ya fusata matuka da rubutun da daya daga cikin wani hadimansa ya yi.

Gwamnan ya dakatar da Mr Wale Ajetunmobi daga mukaminsa na musamman bayan wallafa bayanai marasa tushe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262