Bola Tinubu da Uwar Gidarsa Sun Kama Hanya, Sun Lula Ƙasar Faransa

Bola Tinubu da Uwar Gidarsa Sun Kama Hanya, Sun Lula Ƙasar Faransa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu da uwar gidarsa, Oluremi Tinubu sun tafi ziyarar aiki ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai
  • Hadimin shugaban kasa kan harkokin soshiyal midiya, Dada Olusegun ya tabbatar da Tinubu da twagarsa sun bar Abuja
  • Ana sa ran wannan ziyara ta kwanaki uku za ta fi maida hankali ne kan inganta alaƙar kasashen biyu a bangarori da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da uwar gidarsa, Sanata Oluremi Tinubu sun tafi ziyarar aiki kasar Faransa yau Laraba, 27 ga watan Nuwamba.

Tinubu da matarsa sun tafi wannan ziyara ne bisa gayyatar shugaban ƙasar Faransa, Emmanuel Macron da mai ɗakinsa Brigitte Macron.

Bola Tinubu da matarsa.
Shugaba Tinubu da uwar gidarsa sun tafi ziyara ƙasar Faransa Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Bola Tinubu ya tafi kai ziyara a Faransa

Mai taimakawa shugaban ƙasa na musamnan kan harkokin soshiyal midiya, Olusegun Dada ne ya tabbatar da hakan a shafin X yau Laraba.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP ta dakatar da dan majalisa, ta fadi laifinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana sa ran Macron zai tarbi Shugaba Tinubu da mai ɗakinsa a gidan tarihi na rundunar sojin kasar mai shekaru 350.

Haka nan kuma shugabannin biyu za su tattauna a taruka daban-daban kan muhimman batutuwa da uka shafi alaƙar kasashen guda biyu.

Abubuwan da Tinubu zai yi a kasar Faransa

A wannan ziyara ta kwanaki uku, Tinubu da Macron za su tattauna kan inganta dangantakar siyasa, tattalin arziki, da al’adu tsakanin ƙasashen biyu.

Har ila yau shugabannin biyu za su gana domin lalubo hanyoyin samar da ƙarin damarmaki musamman a fannin noma, ilimi, kiwon lafiya da sha'anin tsaro.

Uwar gidar shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu za ta tattauna da mai ɗakin shugaban Faransa Brigitte Macron kan al'amuran da suka shafi tallafawa mata da ƙananan yara.

Manyan ƙusoshin gwamnatin tarayya ne za su raka shugaban ƙasa zuwa wannan ziyara a Faransa.

A bidiyon da wallafa a shafinsa, Dada Olusegun ya tabbatar da cewa jirgin tawagar Bola Tinubu ya tashi daga Abuja.

Kara karanta wannan

Tinubu na shirin tafiya Faransa, jirgin Shettima ya shilla zuwa kasar waje

'Tinubu ya yi watsi da majalisa ya saye jirgi'

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Enyinnaya Abaribe ya yi ikirarin cewa shugaba Bola Tinubu ya sayi sabon jirgin sama ba tare da izinin majalisar tarayya ba

Dan majalisar dattawan daga Abia ta Kudu ya ce babu wata takarda ta neman izinin sayen jirgin da aka gabatarwa majalisar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262