'Yan Daba Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Jami'in Dan Sanda Har Lahira

'Yan Daba Sun Yi Ta'asa, Sun Hallaka Jami'in Dan Sanda Har Lahira

  • Wasu ƴan daba sun ɗauki doka a hannunsu inda suka hallaka wani jani'in ɗan sanda a jihar Adamawa
  • Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da cafke mutum biyu da ake zargi da kisan jami'in tsaron
  • An dai samu rahoton kisan da aka yi wa jami'in ne bayan ɗansa ya miƙa ƙorafi a wajen jami'an ƴan sanda

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Adamawa - Rundunar ƴan sandan jihar Adamawa ta cafke wasu mutane biyu da ake zargi da kashe wani ɗan sanda, mai suna Ibrahim Maizabuwa.

Waɗanda ake zargin, Ezekiel Kefas mai shekara 67 da Stephen Zabadi mai shekara 44, sun fito ne daga gundumar Wamsa Suwa da ke ƙaramar hukumar Lamurde ta jihar.

'Yan daba sun kashe dan sanda a Adamawa
'Yan daba sun hallaka dan sanda a Adamawa Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ƴan sanda sun yi magana kan kisan jami'insu

Jaridar Daily Trust ta ce kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, an kama waɗanda ake zargin ne a ranar 19 ga watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi ta'asa bayan farmakar jami'an 'yan banga a wani hari

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sulaiman Yahayya Nguroje ya bayyana cewa yaron jami'in da ya rasu, Danlami Ibrahim Maizabuwa ne ya kai rahoton lamarin ga ƴan sanda, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Bincike ya nuna cewa an kashe jami’in ne kuma aka birne shi bayan ya ziyarci abokinsa Ezekiel Kefas.

Meyasa aka kashe ɗan sandan?

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Ezekiel Kefas ya yi iƙirarin cewa wasu ƴan daba ne suka kashe jami’in bayan da ya lalata kayayyaki tare da cin zarafin mutane a gidansa.

"Abokina ya zo ya fara lalata kayayyaki da suka haɗa da tukunyar miya da ruwa a gidana yana cin zarafin mutane, a sakamakon haka mata da yara suka nemi ɗauki, wanda ya jawo ƴan daba suka yi masa duka har lahira."

- Ezekiel Kefas

Kwamishinan ƴan sandan jihar, Morris Dankombo, ya bayar da umarnin gudanar da sahihin bincike kan lamarin tare da gurfanar da waɗanda ake zargin.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace ƴan uwan ɗan jarida ana tsaka da jimamin rasuwar mahaifiyarsa

Ƴan sanda sun fafata da ƴan banga

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi ɗauki ba daɗi a tsakanin ƴan banga da jami'an ƴan sanda a jihar Anambra a watan Nuwamban nan.

An yi musayar wutan ne bayan jami'an tsaron sun yi kuskuren cewa suna fafatawa ne da ƴan bindigan ƙungiyar IPOB a ranar Larabar da ta wuce.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng