Tinubu Na Shirin Tafiya Faransa, Jirgin Shettima Ya Shilla Zuwa Kasar Waje

Tinubu Na Shirin Tafiya Faransa, Jirgin Shettima Ya Shilla Zuwa Kasar Waje

  • Mataimakin shugaban ƙasan Najeriya, Kashim Shettima, ya tafi Cote d'Ivoire domin halartar taron SIREXE na shekarar 2024
  • Kashim Shettima zai halarci taron ne domin ya amsa gayyatar da mataimakin shugaban ƙasar Cote d'Ivoire, ya yi masa
  • Tafiyar na zuwa ne bayan shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa ke shirin tafiya zuwa ƙasar Faransa da ke nahiyar Turai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bi sahun shugaba Bola Tinubu wajen ficewa daga Najeriya.

Kashim Shettima ya tashi daga Abuja zuwa birrnin Abidjan, na ƙasar Cote d’Ivoire, domin halartar taron SIREXE na 2024 a ranar Laraba.

Shettima ya tafi Cote d'Ivoire
Kashim Shettima ya tafi kasar Cote d'Ivoire Hoto: @StanleyNkwocha
Asali: Facebook

Babban mataimaki na musamman ga shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, ofishin mataimakin shugaban ƙasa, Stanley Nkwocha, shi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu da uwar gidarsa sun kama hanya, sun lula ƙasar Faransa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kashim Shettima ya tafi ƙasar Cote d'Ivoire

Stanley Nkwocha ya ce ana gudanar da taron ne daga ranar 27 ga watan Nuwamba zuwa 2 ga Disamba 2, a cibiyar baje koli ta birnin Abidjan.

Ya bayyana Kashim Shettima ya halarci taron ne bisa gayyatar mataimakin shugaban ƙasar Cote d'Ivoire, Tiémoko Koné.

Stanley Nkwocha ya ce Shettima zai yi amfani da taron ne wajen bayyana gogewar da Najeriya ta samu a fannin haƙo fetur da makamashi.

"Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasa zai dawo Abuja a yau."

- Stanley Nkwocha

Taron SIREXE zaman ƙasa da ƙasa ne wanda gwamnatin Cote d'Ivoire ta shirya.

Karanta wasu labaran kan Kashim Shettima

Kashim Shettima ya magantu kan tattalin arziƙi

Kara karanta wannan

Bayan hana Ganduje, zababben gwamnan Ondo ya gabatar da shaidar cin zaɓe ga Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta bakin Kashim Shettima bayyana matakin da tattalin arzikin Najeriya ke ciki bayan fara ƙaddamar da manufofin Bola Tinubu.

Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya ce abubuwa su na kyau matuka, ganin cewa tattalin arziki ya fara dawowa hayyacinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng