Goodluck Jonathan Ya Gano Matsalar da Ta Hana Najeriya Samun Cigaba
- Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Goodluck Jonathan, ya koka kan rashin haɗin kan da ake fama da shi a ƙasar nan
- Goodluck Jonathan ya bayyana cewa idan har ba a shawo kan matsalar haɗin kan ba, ci gaba ba zai samu ba a Najeriya
- Jonathan ya nuna damuwa kan cewa har yanzu an kasa ɗaukar kai a matsayin ɗaya, bayan shekara sama da 100 da haɗewa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Delta - Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya bayyana cewa babbar matsalar da ke tunkarar Najeriya ta fuskar siyasa ita ce rashin haɗin kai.
Goodluck Jonathan ya ƙara da cewa ci gaba ba zai samu ga ƙasar nan ba, har sai an shawo kan matsalar.
Tsohon shugaban ƙasan ya bayyana hakan ne jiya a garin Effurun na jihar Delta, lokacin da yake jawabi a matsayin shugaban taron ƙungiyar Wellmann, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Goodluck Jonathan ya ba ƴan Najeriya shawara
Jonathan ya ce ya kamata ƴan Najeriya su fahimci amfanin haɗin kai, bayan sama da shekara 100 da haɗewar ƙasar nan.
"Dole ne akwai dalilin da ya sa waɗannan mutanen suka ji cewa haɗa waɗannan ɓangarorin biyu, yankin Kudu da Arewa, zai samar da ƙasa mai kyau."
"Sannan tun daga haɗewar har zuwa yau, ba mu iya bunƙasa kanmu ba, har ta kai ga mun ɗauki kanmu a matsayin ɗaya."
- Goodluck Jonathan
Shugaba Jonathan ya soki ƴan majalisa
Tsohon shugaban ƙasan ya soki ƴan majalisar tarayya kan yadda suke fifita ƙabilunsu fiye da ƙasa.
Jonathan ya bayyana cewa duk da Najeriya tana da abubuwan da za a kira da su a matsayin ƙasa, har yanzu ba ta da haɗin kai wanda muhimmin ginshiƙi ne wajen gina ƙasa.
PDP za ta goyi bayan Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar jami'iyyar adawa ta ƙasa PDP ta bayyana cewa a shirye take ta marawa tsohon shugaban ƙasa, Dr. Goodluck Ebele Jonathan baya a zaɓen 2027.
Ana tunanin PDP ta yi niyyar miƙawa Jonatahn tikiti idan ya amince zai dawo ya yi takarar shugaban ƙasa a babban zaɓe mai zuwa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng