Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Gaban Kotu a Abuja

Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Jihar Kogi a Gaban Kotu a Abuja

  • Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ranar Laraba
  • Wannan na zuwa ne bayan jami'an EFCC sun cafke tsohon gwamnan a Abuja ranar Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024
  • Jami'an EFCC sun musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa Yahaya Bello ne ya miƙa kansa a hedkwatar hukumar da ke Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja.

Yahaya Bello ya shiga hannun EFCC ne jiya Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024 bayan shafe tsawon lokacin yana ɓoye a wani wuri da ba a bayyana ba.

Yahaya Bello a kotu.
Jami'an EFCC sun gurfanar da Yahaya Bello a babbar kotun tarayya da ke Abuja Hoto: @NTANews
Asali: Twitter

Yadda EFCC ta kama tsohon gwamnan Kogi

Kara karanta wannan

A ƙarshe, jami'an EFCC sun kwamushe tsohon gwamnan jihar Kogi a Abuja

Wasu rahotanni sun ce Yahaya Bello ne ya miƙa kansa ga jami'an hukumar EFCC a hedkwatarsu jiya Talata da misalin ƙarfe 12:55 na rana.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma jami'an EFCC sun musanta ikirarin da cewa su suka kama shi bayan samun wasu bayanan sirri, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

EFCC ta ayyana neman tsohon gwamnan ruwa a jallo sakamkon ƙin mutunta gayyatar da ta masa, daga bisani kotu ta ci gaɓa shari'a ba tare da ya kawo kansa ba.

"Mun kama Yahaya Bello" - EFCC

Jami'an EFCC sun bayyana cewa sun cafke Yahaya Bello ne saɓanin rahotannin da ke yawo cewa shi da kansa ya miƙa kansa.

Wani jami'in EFCC da ya nemi a sakaya sunansa ya ce:

"Kuna ganin wannan mutumin (Yahaya Bello) yana da niyyar zuwa kotu ne? Abin da zan iya faɗa maku shi ne jami'anmu na sashin dabaru ne suka yi ram da shi bayan tattara bayanan sirri."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Tsohuwar Minista Ta Sake Komawa Kotu Bayan Tinubu Ya Kore Ta

"Idan mika kansa ya yi kamar yadda ake ikirari kuna ganin ba zai zo tare da Gwamna Usman Ododo ba? Duk wannan jita-jitar da ake yaɗawa ku yi watsi da ita."

EFCC na tuhumar tsohon gwamnan da karkatar da maƙudan kudi a lokacin da yake kujerar gwamnan Kogi, daga ciki har da tuhumar wawure N80.2bn, rahoton Channels tv.

EFCC ta taso tsohon gwamnan Edo

A wani rahoton, kun ji cewa hukumar EFCC na binciken mu'amalolin kudi da kwangiloli da aka bayar a lokacin mulkin tsohon Gwamna Godwin Obaseki.

Bayan sauka daga mulki, Obaseki ya ce ba ya tsoron bincike, yana mai cewa zai ba da hadin kai ga hukumar don fitar da gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262