Daga Zama Minista, Mai Dakin Ojukwu Ta Dage Sai Tinubu Ya Saki Nnamdi Kanu
- Ƙaramar ministar harkokin kasashen waje, Bianca Ojukwu ta ce tana da karfin gwiwar cewa Bola Tinubu zai saki Nnamdi Kanu
- Bianca Ojukwu ta ce sakin Nnamdi Kanu zai taimaka wajen kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a Kudu maso Gasas
- Shugabannin kabilar Ibo sun dade suna rokon gwamnatin tarayya ta saki Kanu da aka kama tun a shekarar 2021 kan zargin ta'addanci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo - Karamar ministar harkokin wajen Najeriya, Bianca Ojukwu ta ce za ta cigaba da rokon Bola Tinubu ya saki Nnamdi Kanu.
Bianca Ojukwu ta ce tana da tabbas a kan cewa Bola Tinubu zai saurari rokon kuma zai saki madugun yan kungiyar IPOB da aka haramta.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Bianca Ojukwu ta yi maganar ne yayin wani taro a jihar Imo a yau Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Minista ta ce Tinubu zai saki Nnamdi Kanu
Ministar harakokin waje, Bianca Ojukwu ta ce tana da tabbas cewa Tinubu ya fahimci amfanin da za a samu idan aka saki Kanu kuma zai sake shi.
Ministar ta bayyana haka ne yayin wani taron tunawa da mai gidanta, Marigayi Dim Chukwuemeka Odumegwu Ojukwu a jihar Imo.
Minista ta ce Sakin Kanu zai taimakawa tsaro
Bianca Ojukwu ta ce sakin Nnamdi Kanu zai taimaka wajen gano masu amfani da rigar neman yanci suna tayar da fitina.
Ministar ta ce mutane a Kudu maso Gabas na zama cikin firgici saboda matsalar tsaro kuma dole su samo mafita.
Kanu: Minista za ta dage da rokon Tinubu
Ministar ta bayyana cewa ba za ta gajiya ba wajen rokon Bola Tinubu a saki jagoran IPOB, Nnamdi Kanu.
Bianca Ojukwu ta kara da cewa ya kamata yan kabilar Ibo su yi watsi da al'adar zaman gida da aka ƙaƙaba musu duk ranar Litinin.
Ta ce Ibo mutane ne da suka shara a harkar kasuwanci kuma zaman gidan na durƙusa musu harkokin yau da kullum.
Kotu ta yi watsi da bukatar Kanu
A wani rahoton, kun ji cewa babbar kotun tarayya a Abuja ta yanke hukunci kan karar da shugaban haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu.
Nnamdi Kanu, wanda gwamnati ke zargi da laifuffukan cin amanar kasa na jagorantar tafiyar Biafra da ke neman ballewa daga Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng