Buhari Ya Gana Abokan da Ya yi Rayuwar Yarinta da Su a Firamare
- Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na cigaba da sada zumunci da abokan da suka yi yarinta da su a shekarun baya
- A ranar Litinin, shugaba Buhari ya gana da wasu daga cikin wandada suka yi makarantar firamare da sakandare da su a Daura
- Tsohon shugaban kasar ya kasance yana ganawa da abokan karatunsa tun a lokacin da yake mulki da bayan saukarsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Katsina - An yabawa shugaba Muhammadu Buhari wajen kiyaye zumunci tsakaninsa da abokansa tun suna yara.
Shugaba Buhari ya karbi baƙuncin abokan karatunsa da suka yi makaranta a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Hadimin Buhari, Bashir Ahmad ya wallafa yadda tsohon shugaban kasar ya gana da abokansa a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya gana da abokansa a Daura
Abokan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari sun kai masa ziyara a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.
Ziyarar na cikin al'adar tsohon shugaban kasar wacce ya fara tun kafin samun mulkin Najeriya a shekarar 2015.
An yabawa shugaba Buhari kan yadda bai yanke alaka da abokansa ba duk da damar shugabanci da ya samu.
"Tsohon shugaban kasa, Muhammadu ya cigaba da kulla alaka da tsofaffin abokansa na makaranta.
Ya rike zumunci tsakanisa da abokansa na makarantar firamare da sakandare kafin hawa mulki, a lokacin mulki da kuma bayan gama mulki."
- Bashir Ahmad
Tsohon hadimin shugaban kasar ya ce Buhari ya gana da abokan karatunsa a 2016, 2017 da kuma 2022.
Sai kuma a ranar Litinin, 25 ga Nuwamban 2024 suka kara haduwa a gidan shugaba Buhari da ke Daura.
An zargi Buhari da magudin zabe a 2019
A wani rahoton, kun ji cewa tsige alkalin alkalan Najeriya, Walter Onnoghen da shugaba Muhammadu Buhari ya yi, ya na cigaba da jawo ce-ce-ku-ce.
Jagoran yan kabilar Ijaw, Edwin Clark ya zargi Muhammadu Buhari da ministan shari'a a lokacinsa da kitsa tsige Onnoghen.
Edwin Clark ya yi zargin cewa Buhari ya tsige alkalin ne domin ya hango alamun zai kawo masa matsala a zaben shekarar 2019.
Asali: Legit.ng