Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)

Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da wakilan al'ummar Najeriya dake zaune a kasar Saudiyya a ranar Talata, 21 ga watan Mayu, 2019.

Yayin takaitacciyar ganawar tasu, wakilan 'yan Najeriya dake zaune a kasar Saudiyya, sun sanar da shugaba Buhari irin aiyukan da kungiyar su da kuma 'yan Najeriya ke yi a kasa mai tsarki.

Jim kadan bayan kammala ganawar tasu, shugaba Buhari ya tashi daga sashen tashin jirgin gidan sarautar Saudiyya dake filin jirgin saman kasa da kasa na sarki Abdul'aziz dake Jeddah.

Bidiyon tasowar shugaba Buhari daga saudiyya:

Buhari ya ziyarci kasar Saudiyya ne domin gabatar da aikin Umrah.

Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)
Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya

Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)
Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya
Asali: Twitter

Buhari ya gana da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya, ya tashi zuwa Abuja (Hotuna da bidiyo)
Buhari na gabatar da jawabi yayin gana wa da 'yan Najeriya mazauna Saudiyya
Asali: Twitter

A daren ranar Litinin ne, Legit.ng ta kawo muku labarin cewar shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha ruwa tare da jagoran jam'iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, da mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, da ragowar wasu manya 'yan Najeriya a kasar Saudiyya.

DUBA WANNAN: Buhari ya yi magana a kan Zamfara yayin shan ruwa da Yari da sarkin Maradun a Saudiyya

Ganawar ta shugaba Buhari da Tinubu da ragowar manyan mutanen na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwanaki kalilan a rantsar da shi a matsayin zababben shugaban kasar Najeriya a karo na biyu.

A cewar jawabin da kakakin shugaban kasa, Garba Shehu, ya fitar, Tinubu ya yi amfani da damar shan ruwa tare da Buhari da ragowar manyan mutanen wajen yin kira ga shugabanni da jagorori a Najeriya su guji yin furucin da kan iya haddasa fitina.

A wurin taron shan ruwan akwai sarkin Kazaure, Najib Hussaini Adamu, da ragowar wasu hadiman shugaba Buhari da wakilan gwamnati dake cikin tawagar shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel