An Kama Barawon Buhunan Shinkafa 150, Ya Sace Kwalayen Taliya 43 da Man Gyada

An Kama Barawon Buhunan Shinkafa 150, Ya Sace Kwalayen Taliya 43 da Man Gyada

  • Rundunar yan sandan Najeriya a jihar Bauchi ta yi nasarar cafke wani matashi da ake zargi da zuwa shaguna yana sace kayan al'umma
  • An kama wanda ake zargi mai suna Ukasha Adamu da tarin buhunan shinkafa, kwalayen taliya, man gyada da sauran kayayyaki
  • Rundunar yan sanda ta bayyana cewa kayan da ya sace sun kai sama da Naira miliyan 13 kuma har yanzu ana cigaba da bincikensa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - Rundunar yan sanda ta kama wani matashi mai suna Ukasha Adamu da zargin sata a shaguna.

An kama matashin mai shekaru 23 da haihuwa dauke da buhunan shinkafa 150 da sauran kayayyakin da ake zargi na sata ne.

Shinkafa
An Kama barawon buhunan shinkafa a Bauchi. Hoto: Nigeria Police Force Bauchi State Command
Asali: Facebook

Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta wallafa yadda ta kama Ukasha Adamu a wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

An kama hatsabibin dan daba da aka ɗauki lokaci ana nema a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kama 'barawon' shinkafa a jihar Bauchi

Yan sandan Najeriya a jihar Bauchi sun cafke wani matashi da ake zargi yana bin shaguna yana sace kayan abinci.

Tribune ta wallafa cewa a ranar 11 ga watan Nuwamba asirin Ukasha Adamu ya tonu yayin da yan sandan sashen bincike na CID suka cafke shi.

Yadda barawon shinkafa ke sata a Bauchi

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa ɓarawon yana zuwa shuguna ne ya lura da irin mabuɗansu sai a hada masa irinsu a makera.

Daga nan kuna sai ya taho shagunan a lokacin da yan kasuwar ba su nan ya bude su ya kwashe kaya a cikin mota ya gudu.

Yan sanda sun bayyana cewa halin ɓera da Ukasha Adamu ke yi yana jawo koma baya a bangaren tattalin arziki da tsaron jihar.

Kayayyakin da aka samu wajen Ukasha

Rundunar yan sanda ta tabbatar da cewa an kama kayayyakin da suka hada da shinkafa da taliya. Ga jerin kayayyakin:

Kara karanta wannan

An kama yan ta'adda da miyagu 523, an ceto mutane 102 a Kaduna

  • Buhunan shinkafa 150
  • Kwalayen taliya 43
  • Katon din man gyada 20
  • Taki na ruwa katon 42

Yan sanda sun bayyana cewa idan aka hada kudin kayayyakin da ya sace sun kai sama da Naira miliyan 13.

An damke wani babban dan daba a Kano

A wani labarin, mun ruwaito muku cewa rundunar yan sanda a jihar Kano ta kama wani ƙasurgumin ɗan daba.

An kama Auwal ɗan daba ne bayan an shafe lokaci ana nemansa saboda laifuffuka da ya aikata da dama musamman a unguwar Ɗorayi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng