An Kama Hatsabibin Ɗan Daba da Aka Ɗauki Lokaci Ana Nema a Kano
- Rundunar yan sandan Najeriya a Kano na cigaba da farautar yan daba da sauran miyagu domin dakile barna a fadin jihar
- Yan sanda sun yi nasarar cafke wani kasurgumin dan daba mai suna Auwalu Aliyu da ya shahara da aikata ta'addanci
- Kakakin rundunar yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da cewa an shafe watanni ana neman dan dabar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Yan Najeriya a jihar Kano na cigaba da ƙoƙarin kakkaɓe miyagu da sauran yan ta'adda.
A ƙoƙarin da jami'an rundunar ke yi, sun cafke wani dan daba da ake nema ido rufe mai suna Auwal Aliyu.
Kakakin yan sandan Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan sanda kama mugun dan daba a Kano
Rundunar yan sanda ta samu gagarumar nasara wajen cafke wani hatsabibin dan daba da ake nema ido rufe.
A ranar Litinin, 25 ga watan Nuwamba yan sanda suka sanar da cafke dan dabar mai suna Auwal Aliyu.
Kakakin yan sandan jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce Auwal Aliyu na ciki jagororin yan daba a Kano. Ga abin da yake cewa:
"Auwal Aliyu dan shekaru 22 da ke unguwar Dorayi, wanda aka fi sani da suna "Auwalu Dan Daba" shi ma ya zo hannu bayan mun kwashe watanni muna farautarsa.
Yana daya daga cikin jagororin daba a unguwar Dorayi."
- Abdullahi Haruna Kiyawa
Al'umma sun yabawa rundunar yan sandan jihar Kano bisa kokarin da suka yi wajen kama dan dabar.
Ana sa ran cewa za a gurfanar da Auwal ɗan Daba a gaban alkali bayan kammala binciken yan sanda.
An kama yan ta'adda 523 a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar yan sandan Najeriya a jihar Kaduna ta fitar da rahoto kan miyagun da ta kama daga watan Oktoba zuwa Nuwamba.
Kwamishinan yan sandan jihar Kaduna ya bayyana cewa sun kama miyagu sama da 500 da kuma ceto mutane sama da 100 da kwato wasu tarin kayyakki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng