Ana Murnar Rage Farashin Feturin Ɗangote, Matatar Man Fatakwal Ta Fara Aiki
- Kwanaki ƙalilan bayan matatar man Ɗangote ta rage farashin litar mai, NNPCL ya sanar da fara aikin matatar Fatakwal
- Mai magana da yawun kamfanin mai na kasa, NNPCL, Mista Femi Soneye ya ce wannan babbar nasara ce ga Najeriya
- Ya taya shugaban ƙasa, Bola Tinubu, NNPCL da tawagar Mele Kyari murna bisa jajircewar da suka yi har aka kawo wannan mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Matatar man Fatakwal, babban birnin jihar Ribas ta fara aikin tace ɗanyen mai bayan tsawon lokaci ba ta aiki.
Babban jami'in sashin sadarwa na kamfanin mai na ƙasa watau NNPCL, Femi Soneye ne ya tabbatar da hakan ga menama labarai.
NNPCL: Matatar Fatakwal ta fara tace ɗanyen mai
Wannan ya kawo ƙarshen surutu da sa ranar fara aikin matatar da gwamnatin tarayya ta yi a lokuta da dama a baya, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Femi Soneye ya ce manyan motoci za su fara jigilar mai a matatar yau Talata, 26 ga watan Nuwamba, 2024, rahoton Daily Trust.
Ya kuma ƙara da cewa kamfanin mai NNPCL na aiki ba dare ba rana domin tashin matatar man Warri nan ba da daɗewa ba.
NNPCL ya ce wannan babbar nasara ce
"A yau mun samu wata babbar nasara a Najeriya yayin da matatar mai ta Fatakwal ta fara aikin sarrafa danyen mai a hukumance.
"Wannan gagarumin ci gaba na nuni da wani sabon zamani na dogaro da kai wajen samar da mai da ci gaban tattalin arzikin ƙasarmu.
"Mu na taya Shugaba Bola Ahmed Tinubu, NNPCL, da tawagar Mele Kyari murna bisa jajircewar da suka yi wajen cimma wannan nasara. A tare za mu sake fasalin makamashi a Najeriya."
- Femi Soneye.
Matatar Ɗangote ta rage farashin fetrur
A wani rahoton, an ji cewa matatar man Aliko Dangote ta dauki matakin rage farashin man fetur ga yan kasuwa domin saukaka musu da yan kasa baki daya.
Matatar ta ɗauki matakin ne domin saukakawa yan kasa da ba yan kasuwa damar samun rarar N20 a kan kowace lita.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng