Gwamnan Sokoto Ya Yi Wa Shugabannin Makarantun Sakandare Gata

Gwamnan Sokoto Ya Yi Wa Shugabannin Makarantun Sakandare Gata

  • Gwamnan jihar Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya amince da biyan kuɗaɗen alawus ga shugabannin makarantun sakandare
  • Alhaji Ahmed Aliyu ya amince a riƙa biyansu kuɗin alawus na N200,000 duk wata domin kula da makarantunsu
  • Za a fara biyan kuɗaɗen ne daga watan Janairun 2025, ga dukkanin makarantun sakandare da ke ƙananan hukumomin jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Gwamnan Sokoto, Alhaji Ahmed Aliyu, ya amince da biyan N200,000 a matsayin alawus ga shugabannin makarantun sakandare na jihar.

Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da biyan kuɗin ne domin kulawa da makarantun sakandaren a faɗin jihar.

Gwamnan Sokoto ya ba da alawus
Gwamna Ahmed Aliyu ya amince da biyan shugabannin makarantun sakandare alawus Hoto: @AhmedAliyuskt
Asali: Twitter

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin taron tattaunawa kan kasafin kuɗin jihar Sokoto na shekarar 2025, wanda aka gudanar a cibiyar nazarin Al-Qur’ani ta Sultan Abubakar Maccido, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kogi ya sake yin nade naden mukamai a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An miƙa ƙoƙon bara gaban gwamnan Sokoto

A nasa jawabin, tsohon mataimakin gwamnan jihar, Chiso Abdullahi, ya roƙi Gwamna Ahmed da ya amince da wasu kuɗaɗe ga shugabannin domin kula buƙatun makarantunsu.

Chiso Abdullahi ya bayyana cewa kuɗaɗen za su taimakawa shugabannin makarantun wajen yin ƴan ƙananan gyare-gyare ba sai sun yi dogon jira kafin amincewar gwamnati ba.

Shugabannin makarantun sakandare za su samu alawus

Da yake mayar da martani a madadin gwamnan, babban sakataren yaɗa labaransa, Abubakar Bawa, ya tabbatar da cewa gwamnan ya amince da ba da N200,000 ga kowace makaranta a ƙananan hukumomi 23 duk wata.

Abubakar Bawa ya bayyana cewa za a fara biyan kuɗaɗen ne a watan Janairun 2025, rahoton jaridar Tribune ta tabbatar.

"Kafin na kira mai magana na gaba, bari na sanar da wannan muhimmin taron cewa gwamna bisa ga roƙon da tsohon mataimakin ya yi, ya amince da biyan N200,000 ga kowane shugaban makaranta duk wata."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Gwamnonin PDP sun aika da sako ga Shugaba Tinubu

"Za a fara biyan kuɗin ne a watan Janairun 2025 kuma za a ba dukkanin makarantun sakandare a faɗin ƙananan hukumomi 23 na jiha."

- Abubakar Bawa

Gwamnan Sokoto ya yi afuwa ga fursunoni

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Sokoto, Ahmed Aliyu, ya yi afuwa ga fursunoni 113 da ke gidan gyaran hali na Sokoto.

Gwamna Ahmed Aliyu ya yi afuwar ne a ranar Talata, 22 ga watan Oktoban 2024 domin tunawa da cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng