Bayan Auren 'Yar Kwankwaso da Dan Mangal, Gwamnati ta Rufe Ofishin Jirgin Max Air a Kano

Bayan Auren 'Yar Kwankwaso da Dan Mangal, Gwamnati ta Rufe Ofishin Jirgin Max Air a Kano

  • Gwamnatin Kano ta rufe babban ofishin Max Air da wasu kamfanoni biyu kan rashin biyan kuɗin haraji na tsawon shekaru
  • Hukumar tattara haraji ta jihar Kano ta ce wannan matakin ya zama dole bayan gano makudan kudin da gwamnati ke bin kamfanonin
  • A cewar hukumar ta ɗauki wannan matakin ne domin babu wani shafaffe da mai da za a kyale ya ƙi biyan haƙƙin gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta rufe wasu kamfanoni kan rashin biyan haraji na tsawon shekaru.

Hukumar tattara kuɗaɗen shiga ta jihar Kano ta rufe kamfanonin ciki har da ofishin kamfanin sufurin jiragen sama na Max Air a yau Litinin.

Gwamna Abba Kabir.
Gwamnatin Kano ta rufe ofishin Max Air da wasu kamfanoni kan haraji Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Kano ta rufe kamfanoni 3

Jaridar Vanguard ta tattaro cewa sauran kamfanonin da aka rufe sun haɗa da kamfanin gine-gine na Dantata and Sawoe Construction da ke kan titin Kano-Zaria.

Kara karanta wannan

Tinubu ya karbo bashin Naira tiriliyan 5.63 daga hannun ƴan kasuwa, ya yi ayyuka 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai kuma kamfanin shinkafa na 'Northern Rice and Oil Milling Nigeria Ltd' da ke Gunduwawa a titin zuwa Hadeija a cikin garin Kano.

Gwamnatin Kano ta biyo kamfanin Ɗantata bashin kudin haraji na shekara biyu; 2021 da 2022 kimanin N241.2m, sai kuma kamfanin Northern Rice da ake bi N600,000.

Da yake zantawa da manema labarai, shugaban sashin kula da basussuka na hukumar, Ibrahim Abdullahi ya ce sun rufe kamfanonin ne saboda ƙin biyan haraji.

Meyasa gwamnatin Kano ta rufe kamfanonin?

Ya ce kotu ta bai wa hukumar umarnin rufe manyan kamfanonin sakamakon sun ƙi zuwa su biya waɗannan kuɗaɗe da ake binsu bashi.

A rahoton Daily Trust, Ibrahim ya ce:

"Mun ɗauki wannan matakin ne domin tabbatar da kowa na biyan harajin da ya rataya a wuyansa a lokacin da ya dace, mun gano wasu da suka ƙi biya."
"Don haka muka rufe kamfanonin domin tilasta masu biyan haraji bayan tura masu saƙonnin tunatarwa amma ba su yi abin da ya dace ba."

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso shugaban PDP na ƙasa da NWC a gaba kan Taron NEC

Ƙanin Kwankwaso ya kai karar Gwamna Abba

A wani rahoton, kun ji cewa ɗan uwan Rabi'u Musa Kwankwaso ya maka Gwamna Abba Kabir a kotu kan takaddamar fili a jihar Kano.

Mutumin mai suna Garba Musa Kwankwaso wanda kani ne a wurin tsohon gwamnan ya bukaci kotun da dakatar da gwamnan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262