Sarki Mafi Daɗewa a Sarauta, Muhammadu Inuwa Ya Rasu Yana da Shekaru 111
- Allah ya yi wa sarkin Beli da ke yankin ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi, Muhammadu Inuwa rasuwa yana da shekara 111
- Basaraken wanda ya shafe shekara 91 a kan sarauta shi ne sarki mafi daɗewa a kan karagar mulki, ya rasu a asibitin FMC
- Babban limamin garin Beli, Liman Musa Abubakar ya bayyana rasuwar sarkin a matsayin babban rashi ga Arewacin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Sarkin da ya fi kowane basarake daɗewa a kan karagar mulki a jihar Bauchi, Alhaji Muhammadu Inuwa ya riga mu gidan gaskiya.
Muhanmadu Inuwa, wanda shi ne sarkin Beli (magajin garin Beli) da ke ƙaramar hukumar Shira a jihar Bauchi ya rasu ne a asibitin FMC da ke garin Azare.
Bauchi: Sarki mafi ɗaɗewa a sarauta ya rasu
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Sarkin Beli ya rasu yana da shekaru 111 a duniya bayan shafe shekaru 91 a kan karagar sarauta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban limamin garin Beli da ke ƙaramar hukumar Shira, Liman Musa Abubakar ya tabbatar da rasuwar sarkin ga manema labarai.
Limamin ya bayyana rasuwar basaraken a matsayin babban rashi ba wai ga jihar Bauchi kaɗai ba, ga Arewacin Najeriya gaba ɗaya.
Sarkin Beli ya faɗi yadda ya hau sarauta
A daya daga cikin hirar da Aminiya ta yi da shi a lokacin rayuwarsa, marigayi Sarkin ya ce:
"Kakanmu ya yi shekara 12 a sarauta, Allah ya masa rasuwa, aka naɗa babanmu a matsayin dagacin Beli, ya yi shekara 17 a sarauta, sannan aka naɗa ni tun ina da shekara 19."
"A lissafi na an haife ni a 1912 ko 1913 kuma sarkin Katagum, AbdulQadir ne ya naɗa ni a sarauta a 1933."
Allah ya ba marigayi sarkin Beli tsawoncin kwana, ya yi aiki da sarakunan Katagum har guda huɗu.
Shugaban JNI a Kaduna ya rasu
A wani rahon, kun ji cewa fitaccen malami kuma shugaban kungiyar Jama’atu Nasril Islam (JNI) ya riga mu gidan gaskiya a jihar Kaduna.
Marigayin mai suna Jafaru Makarfi ya rasu ne a daren ranar Asabar 23 ga watan Nuwambar 2024 yana da shekaru 93.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng