'Yan Bindiga Sun Yi Ta'asa bayan Farmakar Jami'an 'Yan Banga a Wani Hari
- Jami'an tsaro na ƴan banga sun fuskanci wani hari daga wajen ƴan bindiga a jihar Anambra a 'yan kwanakin nana
- Ƴan bindigan sun kai wa ƴan bangan hari a ranar Lahadi, 24 ga watan Nuwamban 2024 inda suka raunata mutum ɗaya
- Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta hannun kakakinta, ta tabbatar da kai harin da ƴan bindigan suka yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - Wasu ƴan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaro na ƴan banga a jihar Anambra.
Ƴan bindigan sun farmaki ƴan bangan ne na yankin Umuchu a kan titin Amesi/Uga.
Tashar Channels tv ta rahoto cewa ƴan bindigan sun raunata mutum ɗaya tare da ƙona motar jami'an tsaron a yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan sanda sun tabbatar da harin
Hukumomin ƴan sandan sun bayyana cewa an kai wa ƴan bangan hari ne a ranar Lahadi, 24 ga watan Nuwamban 2024, rahoton Daily Post ya tabbatar.
A cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ƴan sandan jihar Anambra, Tochukwu Ikenga ya fitar a ranar Litinin, ya bayyana cewa an garzaya da jami'in da ya samu rauni zuwa asibiti.
"Rundunar jami'an tsaro ta haɗin gwiwa ta yi gaggawar kai jami'in zuwa asibiti inda ake ba shi kulawa, sannan ta ƙara tsaurara sintiri a yankin domin hana ƴan bindigan sakewa a ƙoƙarin cafke su."
"Abin takaici, a yayin musayar wutan, harsashi ya samu tankin fetur na mota ƙirar Toyota Frontier ta jami'an ƴan bangan wanda hakan ya jawo ta ƙone."
- Tochukwu Ikenga
Karanta wasu labaran kan ƴan bindiga
- An samu asarar rayuka bayan 'yan bindiga sun farmaki 'yan sanda
- 'Yan bindiga sun hallaka 'yan banga a wani harin kwanton bauna
- 'Karshen Turji da yan bindiga ya kusa': Ministan tsaro bayan karbar jirage daga Turkiyya
Ƴan bindiga sun kai hari a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagerun ƴan bindiga sun hallaka mutum biyar a kauyen Dayau da ke ƙaramar hukumar Ƙaura Namoda a jihar Zamfara ranar Lahadi da daddare.
Rahotanni sun bayyana cewa ƴan bindigan sun ƙona gawarwakin waɗanda suka kashe da shaguna da rumbunan ajiyar kayayyakin abinci a ƙauyen.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng