Gwamnan Kogi Ya Sake Yin Nade Naden Mukamai a Gwamnatinsa
- Gwamnan Kogi, ya yi naɗe-naɗe a hukumar kula da ilmin sakandare ta jihar watanni kusan 10 bayan ya shiga ofis
- Alhaji Ahmed Usman Ododo ya naɗa shugaban hukumar da wasu manyan mambobi yayin da yake jiran majalisar dokoki ta tabbatar da su
- Gwamna Ododo ya buƙace su da su yi amfani da ƙwarewar da suka samu wajen sauke nauyin da aka ɗora musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kogi - Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Ododo, ya yi naɗi a hukumar kula da ilmin sakandare ta jihar.
Gwamna Ahmed Usman Ododo ya amince da naɗin shugaban hukumar kula da makarantun sakandire na jihar Kogi da manyan mambobinta.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakatariyar gwamnatin jihar Kogi, Dr. Folashade Arike Ayoade ta fitar wacce aka sanya a shafin yanar gizo na kogistate.gov.ng
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Ododo ya yi naɗe-naɗen mukamai
A cewar sanarwar, wadanda aka nada sun hada da Dr. Habiba Suleiman a matsayin shugaba, yayin da Paul Peter Jibrin zai wakilci Kogi ta Gabas a matsayin babban mamba.
Sauran wadanda aka nada sun haɗa da Hussaini Ada Alhassan, babban mamba na biyu mai wakiltar Kogi ta Yamma, da Adambe Otaru, mamba mai wakiltar Kogi ta Tsakiya.
Naɗin na su na buƙatar amincewa majalisar dokokin jihar domin tabbatar da su.
Sanarwar ta ci gaba da cewa nadin na daga cikin ƙudirin gwamnati mai ci na bunƙasa ilimin sakandare a jihar.
Gwamna Ododo ya taya waɗanda aka naɗa murnar samun muƙaman, sannan ya buƙace su da su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamnan Kogi zai gina filin jirgin sama
A wani labarin kuma, kun ji cewa ma’aikatar sufurin jiragen sama ta tarayya ta amince bukatar gwamnatin jihar Kogi na gina filin jirgin sama na kasa da kasa da kasa a Zariagi.
Kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 25 ga watan Oktoba.
Kwamishinan ya ce filin jirgin sama na jihar Kogi na da girman da jihohi 10 za su iya amfani da shi wanda zai rage zirga-zirgar ababen hawa a hanyar Lokoja zuwa Abuja.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng