Yan Majalisa Za Su Gwabza kan Bukatar Tinubu na Karɓo Bashin $2.2bn
- Majalisar wakilan kasar nan za ta tattauna bukatar shugaba Bola Ahmed na karbo sabon rancen Naira Tiriliyan 1.77
- An dai ji mataimakin kakakin majalisa, Philip Agbes ya tabbatar da cewa ba za su kawo cikas ga bukatar ba
- Amma alamu sun nuna cewa yan majalisar jam'iyyar adawa za su iya kawo cikas kan bukatar sabon rancen kudin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Akwai alamun za a samu tataburza tsakanin yan majalisar wakilan kasar nan kan sabon bashin Naira Tiriliyan 1.77 da Bola Tinubu ya nema.
Rahotanni sun bayyana cewa akwai sabani mai girma tsakanin yan majalisa karkashin jam’iyyar APC da na jam’iyyar adawa bisa bukatar.
Jaridar Punch ta wallafa cewa mataimakin kakakin majalisa, Philip Agbese ya tabbatar da cewa ba za su ba shugaban Bola Tinubu matsala kan bukatar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa tuni yan majalisa su ka fara yi wa bukatar duba na tsanaki, kuma da zarar sun samu tabbacin za a yi amfani da shi wajen ayyukan raya kasa, za su amince da shi.
Tinubu ya nemi karbo bashin N1.77tn
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya mika bukatar karbo sabon rance ne yayin da kasar nan ke fama niki niki da bashi.
Bola Tinubu ya mika bukatarsa ga majalisar wakilai ta cikin wasikar da ya aika masu, wanda Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Majalisa ta amince da bukatar Tinubu
Majalisar dattawan Najeriya ta riga ta amince da bukatar da shugaban kasa ya aika na karowa kasar nan bashi.
Idan majalisar wakilai ta bi sahun takwararta ta dattawa, za a yi amfani da kudin ne wajen cika kasafin kudin nan da N9.7tn.
Tinubu zai karbo sabon bashi
A baya mun ruwaito cewa majalisar dattawan kasar nan ta amince da bukatar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da ya karbo sabon rancen Naira tiriliyan 1.7 a ranar Alhamis da ta gabata.
Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin basussukan da ake bin kasa a gida da waje, Aliyu Wamakko ne ya tabbatar da haka a rahotonsa bayan Tinubu ya mika bukatarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng