Gwamna Ya Umarci Cafke Wasu Ma'aikatan Lafiya a Jiharsa

Gwamna Ya Umarci Cafke Wasu Ma'aikatan Lafiya a Jiharsa

  • Gwamnan jihar Ebonyi ya samu nasarar yin kaciɓus da wasu ma'aikata da ke karkatar da kayayyakin da gwamnati ta samar
  • Francis Nwifuru ya umarci cafke ma'aikatan tare da gurfanar da su a gaban kuliya bisa zargin yi wa gwamnati sata
  • Ya nuna damuwarsa kan yadda mutanen ke karkatar da kayayyakin da aka samar domin amfanin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ebonyi - Gwamnan jihar Ebonyi, Francis Nwifuru, ya bayar da umarnin cafke Ndukwe Ayansi da wasu ma'aikatan lafiya guda biyar tare da gurfanar da su gaban kuliya.

Gwamna Nwifuru ya ba da umarnin ne bisa zarginsu da karkatar da kayayyakin da aka tanada a ma’aikatar lafiya ta jihar.

Gwamnan Ebonyi ya umarci cafke wasu ma'aikata
Gwamna Francis Nwifuru ya umarci cafke wasu ma'aikatan lafiya Hoto: @FrancisNwifuru
Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Monday Uzor, ya fitar a ranar Lahadi, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kara yi wa ma'aikata karin albashi bayan amincewa da N70,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Nwifuru ya yi kiciɓus da ɓarayi

A cewar Monday Uzor, gwamnan yayin fita duba ayyukan da ake yi, ya yi kaciɓus da mota ɗauke da littafai da sauran kayayyaki daga wajen ajiyar ma’aikatar lafiya da ke Abakaliki, babban birnin jihar, rahoton The Punch ya tabbatar.

Gwamna Nwifuru wanda ya shiga ya yi bincike amma bai gamsu ba, ya ƙara zurfafawa inda ya gano cewa an ɗauko rajistar bayanan marasa lafiya, katuna da wasu tarin takardu a cikin motar.

Nwifuru ya koka kan halin gurɓatattun ma'aikata

"Kuna sayar da takardun gwamnati ba tare da izini ba a ranar Asabar da yamma."
"Asibitocin mu da ke yankunan karkara suna neman rajista da fom din shigar da bayanai da katunan asibiti. Abin baƙin ciki, waɗanda gwamnati ta samar, ku na sayar da su."

- Francis Nwifuru

A halin da ake ciki, ƴan sanda sun kama waɗanda ake zargin yayin da ake ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Bauchi: Gwamna zai fara biyan sabon albashi da hakkokin ma'aikata

Gwamna Nwifuru ya kulle gidajen mai

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin Ebonyi ta samu wasu gidajen mai guda uku a babban birnin jihar, Abakaliki da yi wa jama'a ɗangwashe, duk da tsadar da fetur ya yi.

Gwamnan jihar, Francis Nwifuru ya bayyana cewa ba za su saurarawa duk wadanda aka kama da kara jefa jama'a a cikin kuncin rayuwa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng