Sanata Barau Ya Ja Kunnen Masu Aikata Laifuka bayan ba 'Yan Sanda Babura a Kano

Sanata Barau Ya Ja Kunnen Masu Aikata Laifuka bayan ba 'Yan Sanda Babura a Kano

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya aika da saƙon gargaɗi ga masu aikata laifuka a jihar Kano
  • Sanata Barau Jibrin ya gargaɗi masu aikata laifukan da su tuba su rungumi zaman lafiya ko su fuskanci fushin hukuma
  • Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya yi gargaɗin ne wajen ba da kyautar babura 1,000 ga rundunar ƴan sandan jihar Kano

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ja kunnen masu aikata laifuka a Kano.

Sanata Barau ya gargaɗi masu aikata laifukan kan cewa ba su da sauran wata mafaka domin ƴan sanda na da kayan aikin da za su riƙa sintiri lungu da saƙo a jihar.

Barau ya gargadi masu aikata laifuka a Kano
Sanata Barau ya bukaci masu aikata laifuka a Kano su tuba Hoto: @barauijibrin
Asali: Twitter

Sanata Barau ya bayyana hakan ne a hedkwatar rundunar ƴan sanda ta Kano wajen miƙa babura 1,000 ga CP Salman Garba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake da wasu mutane 14 a jihar Kaduna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Barau ya gargaɗi masu aikata laifuka a Kano

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa gwamnati a jajirce take wajen inganta harkokin tsaro.

Ya buƙaci masu aikata laifuka da su yi watsi da miyagun ayyukansu ko su fuskanci fushin doka.

"Masu aikata laifuka ku shiga taitayinku. Ku daina miyagun ayyukanku ku rungumi zaman lafiya. Rundunar ƴan sandan Kano a shirye take ta isa kowane lungu da saƙo na jihar nan."
"Da waɗannan baburan, za su iya bin ku duk inda kuka yi ƙoƙarin ɓoyewa."

- Sanata Barau Jibrin

Baburan waɗanda aka bayar da su domin inganta ayyukan rundunar ƴan sandan na daga cikin ƙoƙarin da Sanata Barau ke yi domin bunƙasa tsaro.

Barau ya karɓi ƴan NNPP zuwa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata Barau Jibrin ya sake sharewa jam'iyyar APC hanyar lashe zabe a jihar Kano da ya karbi kusoshin NNPP da suka sauya sheka.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ke yi don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

Ɗaruruwan jiga-jigan jam’iyyar NNPP ciki har da hadiman gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da magoya bayansa ke tururuwar komama APC.

Sanata Barau ya ba su tabbacin cewa APC ta na da girman da za ta dauki kowa kuma za a yi musu adalci da mutuntawa kamar sauran ƴan jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng