Tsadar Rayuwa: Gwamnonin PDP Sun Aika da Sako ga Shugaba Tinubu

Tsadar Rayuwa: Gwamnonin PDP Sun Aika da Sako ga Shugaba Tinubu

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP sun nuna damuwarsu kan halin da ake a Najeriya sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziƙi
  • Ƙungiyar gwamnonin ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sake duba manufofinsa kan tattalin arziƙi waɗanda suka jefa ƴan Najeriya cikin wuya
  • Gwamnonin sun bayyana cewa za su ci gaba da aiwatar da tsare-tsare a jihohinsu waɗanda za su sanya jama'a su samu sauƙi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Plateau - Ƙungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta bayyana damuwarta kan taɓarɓarewar tattalin arziƙin da al’ummar ƙasar nan ke fuskanta sakamakon manufofin gwamnatin Bola Tinubu da APC.

Gwamnonin na PDP sun yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya sake duba manufofinsa kan tattalin arziƙin Najeriya.

Gwamnonin PDP sun ba Tinubu shawara
Gwamonin PDP sun ba Shugaba Tinubu shawara Hoto: @DOlusegun, @GovernorAUF
Asali: Twitter

Wannan dai na daga cikin bayanan da ƙungiyar ta fitar a bayan kammala taronta da ta gudanar a birnin Jos na jihar Plateau, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ke yi don kawo ƙarshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnonin PDP sun samo mafita

Gwamnonin na jam'iyyar PDP na ganin sake gyara manufofin za su dawo da walwala da jin daɗin ƴan Najeriya.

Ƙungiyar gwamnonin ta kuma jajantawa ƴan Najeriya kan halin da suka tsinci kansu ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin na PDP kuma gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ne ya karanta sanarwar bayan taron.

Wace shawara suka ba Tinubu?

"Ƙungiyar ta jajantawa ƴan Najeriya waɗanda ke shan wuya a ƙarƙashin matsin tattalin arziƙi wanda aka ƙaƙabawa al’ummar ƙasar nan ta hanyar manufofi da matakan gwamnatin tarayya ta APC."
"Ƙungiyar ta yi kira ga shugaban ƙasa da ya gaggauta sake duba manufofin tattalin arziƙi da na kuɗi ta yadda za su dawo walwala da jin dadin ƴan Najeriya."

- Gwamna Bala Mohammed

Ƙungiyar ta jaddada cewa gwamnonin PDP za su ci gaba da aiwatar da manufofi da shirye-shiryen da za su rage wahalhalu da tabbatar da ci gaba a jihohinsu.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Daga karshe PDP ta bayyana matsayarta kan nasarar APC

Tinubu ya dawo Najeriya

A wani labarin kuma,.kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya iso gida Najeriya daga ƙasar Brazil.

Shugaba Bola Tinubu ya dawo Najeriya daga ƙasar Brazil ne bayan ya halarci taron shugabannin ƙasashen G20.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng