Sanata Barau Ya Bi Sahun Gwamna Abba, Ya Yi Wa 'Yan Sanda Gata a Kano
- Mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya ya gwangwaje rundunar ƴan sanda jihar Kano da babura domin inganta ayyukansu
- Sanata Barau I. Jibrin ya ba da tallafin babura guda 1,000 ga rundunar ƴan sandan jihar Kano a ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamban 2024
- Ko a shekarar 2023, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ba da gudunmawar motoci guda 23 ga rundunar ƴan sandan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau I. Jibrin ya ba rundunar ƴan sandan jihar Kano gudunmawar babura.
Sanata Barau I Jibrin ya ba da tallafin babura guda 1,000 ga rundunar ƴan sandan ta jihar Kano.
Sanata Barau ya gwangwaje ƴan sanda a Kano
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an gudanar da bikin ba da baburan ne a ranar Asabar a ofishin ƴan sanda da ke Bompai, Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ba da baburan ne domin tallafawa jami’an tsaron inganta ayyukansu wajen samar da ingantaccen aikin ƴan sanda a jihar.
Sababbin baburan an ƙera su ne domin amfani kan tituna da kuma aiki a kowane irin yanayin da ake ciki.
A shekarar 2023 Sanata Barau ya ba da gudunmawar motocin aiki guda 22 ga rundunar ƴan sanda.
Barau ya yi ƙoƙari
Ibrahim Zulkiful wanda ke zaune a cikin birnin Kano ya shaidawa Legit Hausa cewa sanatan ya yi ƙoƙari wajen raba baburan ga rundunar ƴan sanda.
Sai dai, ya ce ba ya tunanin baburan za su taimaka wajen samar da tsaro.
"Eh gaskiya ya yi ƙoƙari domin ko ba komai ƴan sanda za su samu sauƙin zirga-zirga. Amma ba na tunanin hakan zai taimaka wajen samar da tsaro."
- Ibrahim Zulkiful
Gwamna Abba ya ba ƴan sanda motoci
Raba baburan dai na zuwa ne bayan kwanakin baya, Gwamna Abba Kabir na jihar ya raba motocin aiki ga rundunar ƴan sandan.
Gwamnan ya ba da motoci guda 78 ga rundunar ƴan sandan waɗanda za a raba su ga ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Abba ya kuma bayyana cewa shirin tallafin ba shi da wata alaka da siyasa, kuma ya yi shi ne kawai domin tabbatar da tsaron mutanen jihar Kano.
Sanata Barau ya tarbi ƴan NNPP a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan takarar kujerar kansila daga ƙaramar hukumar Gwarzo, jihar Kano sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a kasa.
Sanata Barau Ibrahim Jibrin, mataimakin shugaban majalisar dattawa ne ya sanar da ficewar 'yan takarar kansilar daga NNPP zuwa APC.
Asali: Legit.ng