Gobara Ta Tashi a Asibitin Koyarwa na LAUTECH, Dukiya Mai Yawa Ta Kone
- An shiga jimami a asibitin koyarwa na jami'ar Ladoke Akintola (LAUTECH) da ke Ogbomoso a jihar Oyo ta yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
- Wata gobara ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar a asibitin inda ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa ta miliyoyin Naira
- Jami'in hulɗa da jama'a na asibitin ga tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ƙara da cewa an ci gaba ɗa gudanar da harkokin yau da kullum bayan tashin gobarar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Oyo - An samu tashin gobara a asibitin koyarwa na jami'ar Ladoke Akintola (LAUTECH), da ke Ogbomoso a jihar Oyo.
Gobarar wacce ta tashi da sanyin safiyar ranar Asabar, ta jawo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Majiyoyi sun bayyana cewa gobarar ta shafi sashin kula da ba da agajin gaggawa da hadurra na asibitin, cewar rahoton jaridar Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobara ta yi ɓarna a asibitin LAUTECH
Hakazalika, wasu kayan ofis, littattafai, na'urorin lantarki, rufi da silin suma sun kama da wuta a yayin tashin gobarar.
Shaidun gani da ido sun ce gobarar ta auku ne da misalin ƙarfe 5:00 na safe, inda ake zargin gobarar ta tashi ne sakamakon tsartsatin wutar lantarki daga wani ofishi, rahoton The Nation ya tabbatar.
Domin kaucewa asarar rayuka, hukumomin asibitin sun yi gaggawar fitar da majinyata 16 daga sashin a lokacin da gobarar ta tashi.
Me hukumomi suka ce?
Jami’in hulɗa da jama’a na asibitin, Omotayo Ogunleye wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce komai ya dawo daidai a yanzu.
"Eh gaskiya ne. Wani ƙaramin lamari ne amma an dawo gudanar da harkokin yau da kullum a asibitin."
- Omotayo Ogunleye
Gobara ta tashi a kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata mummunar gobara ta lalata dukiyar miliyoyin Naira a babbar kasuwar Laranto da ke karamar hukumar Jos ta Arewa, jihar Filato.
Rahotanni sun nuna kasuwar ta daɗe tana fama da tashin gobara lamarin da ya dade yana ci wa ƴan kasuwar tuwo a ƙwarya.
Mutanen da ke kusa da kasuwar sun yi kokarin kai dauki inda gobarar ta tashi domin kashe wutar, sai dai lamarin ya fi karfinsu.
Asali: Legit.ng