Mutane Sun Dauki Doka a Hannunsu, Sun Bankawa Masu Karbar Kudin Haraji Wuta
- Wasu fusatattun mutane sun ɗauki doka a hannunsu yayin da suka bankawa wasu masu karɓar kuɗaɗen shiga wuta a Anambra
- An cinnawa mutanen wuta ne bayan sun jawo wani mutum ya rasa ransa a ƙoƙarin karɓar kuɗi wajen wani direba
- Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ta ce mutum biyu ne aka bankawa wuta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Anambra - An samu hargitsi bayan wasu fusatattun mutane sun banka masu karɓar kuɗaɗen shiga wuta a jihar Anambra.
Mutanen dai sun banka musu wuta ne bayan sun jawo asarar ran wani mutum da ke bakin titi.
An bankawa masu karɓar haraji wuta
Jaridar The Nation ta rahoto cewa lamarin ya auku ne a ƙarshen mako a hanyar tsohuwar kasuwa, kusa da titin Venn a Egerton.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar shaidun gani da ido, lamarin ya auku ne a lokacin da jami’an suka yi kokawa da wani direban babbar mota wajen karɓe sitiyarinsa.
Direban ya rasa yadda zai yi, lamarin da ya sa motar ta ƙwace sannan ta bugi wani mutum da ke bakin titi.
Mutanen da ke wajen da suka haɗa da masu tuƙa keke Napep, sun hana jami’an tserewa daga wurin da lamarin ya faru, inda suka ɗauki doka hannunsu.
Sun lakadawa jami’an duka da abubuwa daban-daban kafin su banka musu wuta.
Ƴan sanda sun yi bayani
Rundunar ƴan sandan jihar Anambra ta bakin kakakinta, Tochukwu Ikenga ta tabbatar da faruwar lamarin.
"An samu tashin hankali a Onitsha yayin da fusatattun mutane suka bankawa masu karɓar kuɗaɗen shiga mutum biyu wuta, yayin da wasu guda huɗu suka samu suka tsere."
- Tochukwu Ikenga
Gwamna ya yi hawaye wajen birne sanata
A wani labarin kum, kun ji cewa gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya zubar da hawaye a wurin jana'izar marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ranar Juma'a, 22 ga watan Nuwamba.
Gwamna Soludo ya gaza riƙe alhinin da yake ciki har sai da ya yi kuka a wurin birne marigayin a cocin St. Peter Claver Parish, Umuanukam da ke Otolo Nnewi.
Asali: Legit.ng