"Babu Gudu babu Ja da Baya," NLC Ya Gargaɗi Gwamnoni kan Sabon Mafi Karancin Albashi

"Babu Gudu babu Ja da Baya," NLC Ya Gargaɗi Gwamnoni kan Sabon Mafi Karancin Albashi

  • Kungiyar kwadago watau NLC ta ce wa'adin da ta gindayawa gwamnoni kan fara biyan sabon mafi karancin albashi yana nan daram
  • NLC dai ta yi barazanar shiga yajin aiki daga ranar 1 ga watan Disamba idan gwamnoni suka gaza biyan sabon albashin a ƙarshen Nuwamba
  • Mai magana da yawun NLC na ƙasa, Benson Upah ya ce wa'adin da suka bayar yana nan har yanzun babu abin da ya sauya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta gargaɗi gwamnoni cewa wa'adin da ta ba su kan batun biyan sabon mafi karancin albashi yana nan daram.

NLC ta bayyana cewa ba gudu ba ja da baya za ta sa kafar wando ɗaya da duk gwamnan da ya gaza fara biyan sabon albashin a ƙarshen watan Nuwamba, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Buni ya amince da sabon mafi karancin albashi, ya fadi lokacin fara biya

Yan kwadago.
NLC ta jaddada wa'adin da ta ba gwamnoni kan biyan sabon mafi ƙarancin albashi Hoto: Nigeria Labour Congress
Asali: Twitter

Mai magana da yawun kungiyar NLC, Benson Upah, shi ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya aike wa wakilin jaridar Punch a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mafi ƙarancin albashi: NLC ta yi barazana

Idan baku manta ba ƙungiyar NLC ta bai wa gwamnatocin jihohi wa’adin ranar 1 ga Disamba, 2024, su tabbatar sun aiwatar da sabon mafi karancin albashi.

Ƙungiyar ta umarci dukkan rassanta na jihohi su shirya shiga yajin aiki daga ranar 1 ga watan Disamba, matukar gwamnonin suka gaza ƙarin albashin.

Wannan ya sa galibin jihohi suka duƙufa ɗaukar matakan da suka dace da tsare-tsare domin aiwatar da sabuwar dokar albashin kafin karewar wa'adin.

Sai dai har yanzun akwai jihohin da ba su sanar da adadin da za su fara biyan ma'aikata a matsayin sabon albashi mafi kankanta da lokacin da za su aiwatar ba.

Ƙungiyar NLC na nan kan bakarta

A wani gajeren saƙo, kakakin NLC na ƙasa ya jadadda cewa wa'adin da suka gindayawa jihohin yana nan kuma ba gudu ba aja da baya.

Kara karanta wannan

Gwamnoni sun taso shugaban PDP na ƙasa da NWC a gaba kan Taron NEC

"Eh, wa'adin da muka gindaya yana nan, babu abin da ya sauya," in ji Benson Upah.

Wani ma'aikacin gwamnati, Nura Abdullahi ya shaidawa Legit Hausa cewa ya kamata NLC ta ɗauki mataki mai tsauri kan wasu gwamnoni kan albashi.

Ya ce duk da sabon albashin ba zai ɗauki ma'aikaci a wata amma suna bukatar ƙarin albashi saboda halin tsadar rayuwar da ake ciki.

"Ina goyon bayan NLC, mun shirya rufe wuraren aiki saboda wasu gwamnonin ba su da shirin aiwatar da sabon mafi karancin albashin nan."
"Ƙarin nan fa bai taka kara ya karya ba, N70,000 ko buhun shinkafa ba zai saya maka ba ga kudin makarantar yara da ɗawainiya, haba ina ake so mu sa kanmu "

NLC ta ba gwamnatoci shawara

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar kwadago ta bukaci gwamnatoci a matakai daban daban da su fitar da shirye shirye domin tallafawa talakawan Najeriya.

Shugaban kwadago ya bayyana cewa a yanzu haka yan Najeriya na fama da matsananciyar yunwa da ya kamata a tausayawa musu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262