Ifeanyi Ubah: Gwamna Ya Zubar da Hawaye a Wurin Birne Sanatan da Ya Rasu

Ifeanyi Ubah: Gwamna Ya Zubar da Hawaye a Wurin Birne Sanatan da Ya Rasu

  • Gwamnan Anambra ya yi jimamin mutuwar Sanata Ifeanyi Ubah a wurin bikin birne shi ranar Jumu'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024
  • Charles Soludo ya zubar da hawaye a lokacin da yake tuna tattaunawarsa ta karshe da marigayin, ya ce ko kaɗan ba su kawo mutuwa ba
  • Bishop Peter Cardinal Okpaleke ya ce ya kamata mutuwar Sanata Ubah ta zama darasi ga mutane

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Charles Soludo ya zubar da hawaye a wurin jana'izar marigayi Sanata Ifeanyi Ubah ranar Juma'a, 22 ga watan Nuwamba.

Gwamna Soludo ya gaza riƙe alhinin da yake ciki har sai da ya yi kuka a wurin birne marigayin a cocin St. Peter Claver Parish, Umuanukam da ke Otolo Nnewi.

Gwamna Soludo.
Gwamna Charles Soludo ya nuna alhini a wurin jana'izar Sanata Ifeanyi Ubah Hoto: Charles Chikwuma Soludo
Asali: Facebook

The Nation ta ce da yake ba da labarin hirarsu ta karshe a watan Mayu, Soludo ya ce ko kaɗan ba su taɓa kawo sanatan zai mutu a wannan lokaci ba.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa manufofin Shugaba Tinubu suka kawo wahala da tsadar rayuwa a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Soludo ya tuna hirarsu ta karshe

Ya ƙara bayyana kaɗuwa da takaicin mutuwar Ifeanyi Ubah, wadda ya ce ta zo masa kamar a mafarki.

Farfesa Soluso ya ce:

"Har yanzu ina tunawa da hirarmu ta ƙarshe lokacin da na tambaye shi ko yana da buri, kuma ya bani amsa da cewa yana son ba da gudummuwa, ko kaɗan ba mu kawo mutuwa ba a hirarmu."

Gwamna Soludo ya yi alhinin mutuwar kwatsam da sanatan ya yi, sannan ya kara miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai, al'ummar Nnewi da Anambra baki ɗaya.

'Mutuwar Ifeanyi Ubah darasi ce'

A wurin bikin jana'izar, Bishof na Ekwulobia, Peter Cardinal Okpaleke, ya bayyana rasuwar Sanata Ubah a matsayin darasi ga mutane.

"Ya zama dole mu dage mu aikata alheri domin barin abin da za a riƙa tunawa da mu," in ji shi yayin da yake yabawa da halayen Ifeanyi Ubah.

Kara karanta wannan

"Alakar Wike da Tinubu ba ta dame mu ba," Sanata Abba ya faɗi abin da PDP ta sa a gaba

Gwamnan Anambra ya rufe makarantu

A wani rahoton, an ji cewa Gwamna Soludo na jihar Anambra ya ba da hutun makarantu a yankin Nnewi yayin da ake shirin jana'izar Sanata Ifenyi Uba.

Charles Soludo ya umarci shugabannin makarantun yankin su ba ɗalibai hutu daga nan zuwa ranar Talatar mako mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262