Abin da Bola Tinubu Ke Yi Don Kawo Karshen Rikicin Manoma da Makiyaya a Najeriya

Abin da Bola Tinubu Ke Yi Don Kawo Karshen Rikicin Manoma da Makiyaya a Najeriya

  • Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen jawo masu zuba jari a ɓangaren kiwo domin magance rikicin manoma da makiyaya
  • Shugaban ƙasar ya faɗi hakan a wurin ratttaɓa hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin sarrafa nama a ƙasar Brazil
  • Rkicin manoma da makiyaya na ɗaya daga cikin ƙalubalen tsaron da Najeriya ke fama da su wanda ya laƙume rayuka da dama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa gwamnatinsa ta himmatu wajen kawo karshen rikicin manoma da makiyaya a Najeriya.

Rikicin manoma da makiyaya wanda ya samo asali daga ruwa da amfanin gona ya laƙume rayuka da yawa a wasu jihohin Najeriya.

Bola Tinubu.
Shugaba Tinubu ya bayyana kokarin da gwamnatinsa ke yi don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya Hoto: @aonanuga1956
Asali: Twitter

Ana ganin wannan rikici da har yau ya ƙi ƙarewa na neman zama barazana ga harkokin noman abinci a ƙasar nan, kamar yadda Channels tv ta kawo.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya kara yi wa ma'aikata karin albashi bayan amincewa da N70,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu na kokarin magance rikici

Shugaba Tinubu ya ce gwamnatinsa ta maida hankali wajen jawo masu zuba jari a ɓangaren kiwo da nufin warware rikicin, fatattakar yunwa da talauci a Najeriya.

Tinubu ya faɗi haka ne a birnin birnin Rio na kasar Brazil yayin rattaba hannu kan wata takardar yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ta kulla da kamfanin JBS.

Kamfanin JBSS. A n adaya daga cikin manyan kamfanonin sarrafa nama guda uku na sahun farko a duniya.

Wane koƙarin Tinubu ke yi kan rikicin makiyaya?

Shugaban ƙasar ya ce:

"Abin da muke yi a yanzu shi ne ƙoƙarin magance matsalar da ta addabi al'umma a Afirka watau rikici tsakanin manoma da makiyaya wanda ya laƙume rayukan dubban mutane."
 "Muna ƙoƙarin sauya rikici da faɗace-faɗacen da ake yawan yi zuwa yanayin zaman lafiya da samun kofofin bunƙasa tattalin arziki, duk matsalolinmu za su kau, hasken da ke tattare da kiwo zai bayyana."

Kara karanta wannan

Majalisar Dattawa ta amince Bola Tinubu ya karɓo bashin Naira tiriliyan 1.77

Tinubu ya roki kamfanin ya shigo Najeriya

Bola Tinubu ya roki kamfanin da ya duba dumbin danarmakin zuba hannun jarin da ke akwai a ɓangaren kiwo a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya shaida wa manyan jagororin JBS cewa Nijeriya a shirye take ta yi kasuwanci da su, inda ya ba su tabbacin samun riba mai gwaɓi ida suka zuba jari.

Majalisa ta amince Tinubu ya karɓo bashi

A wani rahoton, an ji cewa majalisar dattawan Najeriya ta amince shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya karɓo baahin Naira tiriliyan 1.76 daga waje.

A zaman ranar Alhamis, 21 ga watan Nuwamba, majalisar ta amince da bukatar ne bayan ta karɓi rahoton kwamitin kula da basussukan gida da na waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262