Bello Turji Ya Karbi Kudin Fansar N6m daga Kauyen Sakkwato
- Mutanen kauyen Sakkwato guda biyar sun shaki iskar yanci bayan shafe wani lokaci a hannun yan ta'addan Turji
- Mutanen kauyen Sardauna na karamar hukumar Sabon Gwari sun bayyana cewa sun hada kudin fansar da Turji ya nema
- Tun da fari, mutanen sun bayyana cewa jagoran yan ta'addan ya nemi sama da Naira miliyan shida, amma aka karkare a N6m din
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Sokoto - Kasungurmin dan ta'adda, Bello Turji ya karbi harajin Naira miliyan 6 da ya dorawa mazauna Sardauna a jihar Sakkwato.
An gano jagoran yan ta'addan ya dorawa mutanen Sardauna da ke karamar hukumar Sabon Birni da ke jihar Sakkwato fansar bayan garkuwa da wasu mutane.
Zagazola Makama ya wallafa a shafinsa na X cewa mutanen kauyen sun yi tattaki da kafarsu wajen kai kudin da Bello Turji da yaransa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin ba Bello Turji kudin fansa
Rahotanni sun bayyana cewa mayakan Bello Turji sun yi garkuwa da wasu yan kauyen Sardauna guda biyar domin neman a biya fansa.
Yan kauyen sun bayyana cewa sai da aka rika fafatawa wajen farashin da Turji zai karba kafin a sako mutanen da aka kama.
Turji ya saki mutanen da ya kama
Wasu mazauna Sardauna a Sakkwato sun tabbatar da cewa Bello Turji ya saki mutanensu da aka rike bayan biyan N6m a matsayin fansa.
Wannan na zuwa duk da ikirarin gwamnatin tarayya na cewa ta na fatattakar yan ta'adda, har da mutanen Bello Turji domin wanzar da zaman lafiya.
Turji na shan luguden wuta
A baya kun ji cewa rundunar sojojin Najeriya da hadin gwiwar jami'an sa kai a Sakkwato su na musayar wuta da yan ta'addan Bello Turji da da su ka addabi jama'a.
Mutanen yankin sun bayyana cewa sun shafe akalla kwanaki hudu ana arangama tsakanin dakarun gwamnatin Najeriya domin kakkabe miyagun aikin.
Gwamnatin tarayya ta ce za ta dauki matakin magance ayyukan yan ta'adda da su ka takurawa mazauna Arewacin Najeriya da zummar dawo da zaman lafiya.
Asali: Legit.ng