Kotun Kolin Najeriya Ta Soke Dokar Caca da Majalisar Tarayya Ta Amince da Ita
- Kotun koli ta soke amfani da dokar caca ta ƙasa 2005 a dukkan jihohi 36 na Najeriya ban da birnin tarayya Abuja
- Kwamitin alkalai bakwai ƙarƙashin jagorancin Mai shari'a Muhammed Idris ne ya yanke wannan hukuncin ranar Juma'a, 22 ga watan Nuwamba
- Kotun ta bayyana cewa majalisar tarayya ba ta da hurumin yin doka kan abin da ya shafi caca da wasannin sa'a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kotun kolin Najeriya ta soke dokar caca ta kasa ta 2005 da majalisar dokokin kasar ta kafa.
Kwamitin alkalai bakwai na kotun mai daraja ta ɗaya a Najeriya ne suka yanke wannan hukunci da murya ɗaya yau Juma'a, 22 ga watan Nuwamba, 2024.
Kotun ta yanke cewa majalisar dokokin kasar ba ta da hurumin yin doka a kan batutuwan da suka shafi caca da wasannin sa'a, kamar yadda The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ta ce majalisun dokokin jihohi ne kaɗai ke da ikon kafa irin waɗannan dokokin da suka shafi caca a yankunan, amma ba a majalisar tarayya ba.
A hukuncin da ya karanto a harabar kotun ƙoli, Mai Shari'a Mohammed Idris, ya ba da umarni daina amfani da dokar caca a faɗin jihohi 36 a Najeriya.
Ya ce dokar za ta cu gaba aiki ne a babbar birnin tarayya Abuja kaɗai saboda nan ne majalisar dokoki ta ƙasa ke da ikon kafa doka.
Kotun ƙoli ta yanke hukuncin ne a kan karar da jihar Legas da wasu jihohi suka shigar a shekarar 2008.
Karin bayani na nan tafe...
Asali: Legit.ng