N Power: Tinubu Zai Biya Matasa Bashin da Suka Biyo Gwamnatin Buhari

N Power: Tinubu Zai Biya Matasa Bashin da Suka Biyo Gwamnatin Buhari

  • An fara ƙoƙarin ganin gwamnatin tarayya ta biya bashin da matasan Najeriya yan N-Power suka biyo gwamnatin da ta gabata
  • Tawaga da ta hada da bangarorin gwamnati da yan N-Power ta gana a birnin tarayya Abuja domin duba yadda za a biya matasan
  • Legit ta tattauna da wani dan N-Power, Abubakar Salihu domin jin yadda yaji bayan gwamnati ta musu alkawari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An sake sabon kokari domin ganin an biya matasan N-Power bashin da suka biyo gwamnatin tarayya.

An hada tawaga ta musamman domin ganawa da wakilan gwamnatin tarayya kan yadda za a biya kudin.

N power
Gwamnati za ta biya yan N-Power. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, N-Power
Asali: UGC

Daya daga cikin wakilan matasan N-Power, Barista Adeyanju Deji ne ya wallafa yadda tattaunawar ta gudana a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

An samu rabuwar kai a APC kan zargin sakataren gwamnatin Tinubu da ƙabilanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati za ta biya bashin N-Power

An yi wani zama na musamman tsakanin matasan N-Power da wakilan gwamnatin tarayya a Abuja.

Zaman ya mayar da hankali ne kan yadda za a biya matasan da suka biyo gwamnatin tarayya bashi.

An ruwaito cewa matasan da suke neman hakkinsu su ne yan rukunin C II da suka yi aiki daga watan Oktoba, 2022 zuwa Satumba, 2023.

"A ranar 20 ga watan Nuwamba aka tattauna tsakanin ma'aikatar jin kai da yaki da talauci da matasan N-Power.
Tattaunawar ta kasance kan yadda za a biya yan N-Power bashin da suke bin gwamnati kuma Barista Deji Adeyanju ne ya wakilci bangaren matasan.
Gwamanti ta tabbatar mana da cewa a nan gaba kadan za a biya yan N-Power bashin da suke bin gwamanti."

- Barista Deji Adeyanju

An ruwaito cewa ministan jin kai, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da babban sakataren ma'aikatar sun halarci zaman.

Kara karanta wannan

Zanga zanga : Gwamnatin Kano ta mika yara 76 ga iyayensu, an ba kowane yaro tallafin kudi

Haka zalika shugaba NSIPA, Dr Badamasi Lawal na cikin waɗanda suka tattauna da wakilan matasan.

Legit ta tattauna da Abubakar Salihu

Wani dan N-Power, Abubakar Salihu ya zantawa Legit cewa ba za su cire tsammani daga samun kudin ba, amma kuma ba za su saka buri ba sai sun gani a kasa.

Abubakar Salihu ya bukaci gwamnati ta tausaya musu ta ba su kudin domin saukaka lamuran rayuwa.

Yan N-Powe sun roki Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa matasa ƴan N-Power sun nuna damuwa da shirin gwamnatin tarayya na rusa ma'aikatar harkokin jin kai da yaƙi da fatara.

Shugaban N-Power na jihar Kano, Nazifi Mohammed Abubakar ya ce ma'aikatar ce kaɗai wata hukumar gwamnati mai alaka da talakawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng