Tsohon Gwamna Ya Cika Baki kan Binciken da EFCC Ke Yi Masa

Tsohon Gwamna Ya Cika Baki kan Binciken da EFCC Ke Yi Masa

  • Tsohon gwamnan jihar Delta ya bayyana cewa a shirye yake ya kare kansa kan binciken da hukumar EFCC ke yi a kansa
  • Ifeanyi Okowa ya nuna cewa baya tsoron binciken da hukumar EFCC ke yi kan zarginsa da karkatar da Naira tiriliyan 1.3
  • A kwanakin baya dai hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan ta gayyaci tsohon gwamnan tare da tsare shi kafin daga bisani ta sake shi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Delta - Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya yi magana kan gayyatar da hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta yi masa.

Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa ko kaɗan baya tsoron hukumar EFCC ta bincike shi.

Okowa ya magantu kan binciken EFCC
Ifeanyi Okowa ya ce baya tsoron binciken EFCC Hoto: Dr. Ifeanyi Okowa, EFCC NIgeria
Asali: Facebook

Okowa ya bayyana hakan ne a lokacin da shugabannin yankin Delta ta Arewa ƙarƙashin jagorancin mataimakin gwamna Monday Onyeme, suka kai masa ziyara a gidansa dake Asaba, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan

Gwamna ya cire tsoro, ya bayyana wasu 'ƴan siyasa' da ke ɗaukar nauyin ƴan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me Okowa ya ce kann binciken EFCC?

Ya ce ba ya tsoron abin da ya kira ƙoƙarin wasu ƴan siyasa na ɓata masa suna waɗanda ke adawa da goyon bayansa ga gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori.

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ba shi da wani abin ɓoyewa ko fargaba game da binciken da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawan ke yi, kuma a shirye yake ya kare kansa daga zargen-zargen da ake masa.

Tawagar ta kuma kaɗa ƙuri’ar amincewa da shugabancinsa a lokacin da yake riƙe da muƙamin gwamnan jihar.

EFCC ta gayyaci Ifeanyi Okowa

Makonni biyu kenan da EFCC ta gayyaci Ifeanyi Okowa tare da tsare shi bisa zargin karkatar da Naira tiriliyan 1.3 a lokacin da yake kan mulki.

Bayan an sake shi, tsohon gwamnan yana samun masu zuwa nuna goyon baya daga ƙungiyoyi da shugabanni a jihar.

Okowa ya magantu kan binciken EFCC

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata kan kisan sojoji a jiharsa, ya fadi matakin dauka

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, ya ce ya san mutanen da suka cinno masa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa EFCC ta fara bincikarsa.

Ifeanyi Okowa, wanda ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP a 2023, ya ce ba ya jin tsoron duk binciken da EFCC za ta yi a kansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng