An Yi Rashi: Gwamna Radda Ya Yi Alhinin Rasuwar Basarake a Katsina

An Yi Rashi: Gwamna Radda Ya Yi Alhinin Rasuwar Basarake a Katsina

  • Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa kan rasuwar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi
  • Malam Dikko Radda ya bayyana marigayin a matsayin jajirtaccen ma'aikacin gwamnati wanda ya ba da gudunmawarsa ga Najeriya a ɓangarori daban-daban
  • Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumini Kabir Usman, iyalan marigayin da al'ummar jihar baki ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya yi alhinin rasuwar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi.

Alhaji Ahmadu Kurfi ya rasu ne yana da shekara 93 a duniya.

Gwamna Radda ya yi ta'aziyyar Hakimin Kurfi
Gwamna Radda ya yi alhinin rasuwar Alhaji Ahmadu Kurfi
Asali: Facebook

Gwamna Radda ya yi ta'aziyya

Ta'aziyyar gwamnan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Ibrahim Kaulaha Mohammed, ya sanya a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya kuma miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Sarkin Katsina, iyalan marigayin, masarautar Kurfi da al'ummar jihar Katsina.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Babban Hakimi a Katsina ya rasu yana da shekara 93

Gwamna Radda ya bayyana marigayin a matsayin ma'aikacin gwamnati wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa ƙasa.

Radda ya yabi Ahmadu Kurfi

Gwamnan ya bayyana cewa gudunmawar da marigayin ya ba da wajen aikin gwamnati a Najeriya ta shafi ɓangarori da dama.

"Alhaji Ahmadu Kurfi na daga cikin sahun ma'aikatan da suka hidimtawa Najeriya da sadaukarwa, gaskiya da jajircewa wajen ci gaban ƙasa."
"Gwamna na miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, iyalan Alhaji Ahmadu Kurfi, mutanen Kurfi da gabaɗaya al'ummar jihar Katsina."
"Ya yi addu'ar Allah ya sa Aljannah ta zama makoma ga marigayin ya kuma ba iyalansa haƙurin jure wannan rashin da aka yi."

- Ibrahim Kaula Mohammed

Talban Katsina ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon Darakta-Janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Ambasada Zakari Ibrahim, ya yi bankwana da duniya.

Marigayin wanda ke riƙe da sarautar Talban Katsina a masarautar Katsina, ya rasu ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Disamban 2024 yana da shekara 81 a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng