Kwana Ya Kare: Babban Hakimi a Katsina Ya Rasu Yana da Shekara 93
- An yi rashi na ɗaya daga cikin dattawan ƙasa kuma babban basarake a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya
- Mai riƙe da sarautar Hakimin Kurfi, Alhaji Ahmadu Kurfi, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 93 a duniya
- Marigayin ya taɓa riƙe muƙamin shugaban hukumar zaɓe ta tarayya (FEDECO) wacce ta rikiɗe ta koma INEC a yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Allah ya yi wa babban basarake mai riƙe da sarautar Hakimin Kurfi a jihar Katsina, Alhaji Ahmadu Kurfi, rasuwa.
Hakimin na Kurfi ya rasu yana da shekaru 93 a duniya.
Jaridar Leadeship ta ce marigayin shi ne tsohon shugaban tsohuwar hukumar zaɓe ta tarayya (FEDECO) a Jamhuriyya ta Biyu, wacce daga baya ta koma Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) a yanzu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ne basarake Alhaji Ahmadu Kurfi?
An haifi Alhaji Ahmadu Kurfi a shekarar 1931 kuma har zuwa rasuwarsa yana riƙe da sarautar gargajiya ta ‘Maradin Katsina’ a masarautar Katsina.
Kafin ya fara sarauta, Alhaji Ahmadu Kurfi ya kasance babban ma’aikacin gwamnati a matakin tarayya na tsawon shekaru.
Ya kasance mataimakin babban sakatare a ma'aikatar tsaro lokacin da aka yi juyin mulkin shekarar 1966.
Ya kuma kasance babban sakatare a ofishin shugaban ma'aikata.
Basaraken ya shugabanci hukumar FEDECO
An san Alhaji Ahmadu Kurfi a matsayin shugaba na farko na hukumar FEDECO, wacce sojoji suka kafa domin tsara mulkin farar hula a shekarar 1979.
Hukumar zaɓe ta FEDECO ce ta shirya zaɓen da ya samar da Alhaji Shehu Shagari a matsayin shugaban ƙasan Najeriya.
Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar basarake
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar amininsa a jihar Katsina.
Muhammadu Buhari ya jajantawa iyalan marigayi Talban Katsina kuma tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Ambasada Zakari Ibrahim.
Tsohon shugaban ƙasan ya ce tabbas an yi rashin mutumin kirki da ya ba da gudunmawa sosai wurin tabbatar da inganta tsaro a lokacinsa har ma bayan ya bar aiki.
Asali: Legit.ng