Zaben Gwamna: INEC Ta Mika Takardar Shaidar Lashe Zabe ga Aiyedatiwa

Zaben Gwamna: INEC Ta Mika Takardar Shaidar Lashe Zabe ga Aiyedatiwa

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ba gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, takardar shaidar lashe zaɓe
  • INEC ta kuma ba da irin wannan shaidar ga mataimakinsa, Adelami Oyilade sakamakon nasarar da suka samu a zaɓen gwamnan jihar
  • Lucky Aiyedatiwa ya miƙa godiyarsa ga mutanen jihar kan yadda suka fito suka kaɗa masa ƙuri'a domin ya jagorance su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ba zaɓaɓɓen gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa da mataimakinsa Adelami Olayide takardar shaidar lashe zaɓe.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya lashe zaɓen gwamnan jihar Ondo wanda aka gudanar a ranar Asabar, 16 ga watan Nuwamban 2024.

INEC ta ba Aiyedatiwa satifiket
INEC ta ba Aiyedatiwa shaidar lashe zabe Hoto: @bigmorsh
Asali: Twitter

INEC ta ba Aiyedatiwa satifiket

Kwamishinan INEC na ƙasa reshen jihar Ondo, Farfesa Kunle Ajayi ne ya ba su takardar shaidar lashe zaɓen a Abuja ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Daga karshe PDP ta bayyana matsayarta kan nasarar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na zuwa ne kwanaki huɗu bayan INEC ta ayyana Aiyedatiwa a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan da aka gudanar ranar Asabar.

Gwamna Aiyedatiwa na APC, ya doke Agboola Ajayi na jam’iyyar PDP da wasu ƴan takara 15.

Ya yi nasara a dukkanin ƙananan hukumomi 18 na jihar, inda ya samu ƙuri'u 366,781 fiye da na Agboola Ajayi wanda ya samu ƙuri'u 117,845.

Gwamna Aiyedatiwa ya yi godiya

Da yake jawabi a wajen, Aiyedatiwa wanda ya samu rakiyar gwamnan Ogun, Dapo Abiodun, ya godewa al’ummar jihar Ondo bisa yadda suka fito suka zaɓe shi, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga shugaban ƙasa Bola Tinubu, kan yadda ya tabbatar kowane ɗan takara ya fito ya gwada sa'arsa.

PDP za ta je kotu kan zaɓen Ondo

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen gwamnan jihar Ondo da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba, 2024.

Jam'iyyar PDP ta sha alwashin ƙalubalantar nasarar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam'iyyar APC ya samu a gaban kotu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng