Rikicin Cikin Gida: Matar El Rufai Ta Kalubalanci Danta kan Rigimar Tinubu da Obasanjo

Rikicin Cikin Gida: Matar El Rufai Ta Kalubalanci Danta kan Rigimar Tinubu da Obasanjo

  • Matar tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ta fito shafukan sada zumunta ta ƙalubalanci ɗanta, Bashir El-Rufai
  • Bashir ya yi Allah-wadai da fadar shugaban ƙasa kan sukar da ta yi wa Olusegun Obasanjo kan kalamansa game da shugaba Bola Tinubu
  • Sai dai, Hadiza El-Rufai ta tambaya ko Bashir zai caccaki fadar shugaban ƙasan idan mahaifinsa, Nasir El-Rufai yana cikin gwamnatin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Hadiza El-Rufai, uwargidan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ta ƙalubalanci ɗanta kan sukar fadar shugaban ƙasa saboda caccakar Olusegun Obasanjo.

A baya-bayan nan dai an yi ta ce-ce-ku-ce tsakanin Shugaba Bola Tinubu da tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.

Matar El Rufai ta kalubalanci danta
Rigimar Tinubu da Obasanjo ta sa matar El-Rufai ta kalubalanci danta Hoto: @DOlusegun, @hadizel
Asali: Twitter

An yi musayar yawu tsakanin Obasanjo da Tinubu

Obasanjo dai ya zama babban mai sukar gwamnatin Tinubu, inda ya yi Allah-wadai da manufofinsa na tattalin arziki tare da yin kira da a yi wa hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) garambawul.

Kara karanta wannan

'Ɗa zai gaji ubansa,' Ana so ɗan Shugaba Tinubu ya tsaya takarar gwamnan Legas

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani kan kalaman na Obasanjo, inda ta buƙaci ya dauki lokaci ya yi tunani a kan gazawarsa maimakon sukar duk wata gwamnati da ta samu nasara tun bayan da ya bar mulki a shekarar 2007.

Yadda ta kaya tsakanin iyalan El-Rufai

Da yake mayar da martani kan cacar bakin a shafinsa na X, Bashir El-Rufai, ya ce bai kamata fadar shugaban ƙasa ta riƙa sukar Obasanjo ba, duba da irin hauhawar farashin da ake fama da shi a ƙasar nan.

"Caccakar Obasanjo duk da halin da ƙasar nan ke ciki zai zama ciwon hauka da ya addabi dukkanin ƴan tawagar yaɗa labaran. Hauhawar farashin kayayyaki ya kai kaso 33%."

- Bashir El-Rufai

Sai dai, mahaifiyarsa Hadiza El-Rufai ta yi tambayar cewa Bello zai yi irin waɗannan kalaman da mahaifinsa Nasir El-Rufai yana cikin gwamnatin.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya shilla zuwa waje bayan ganawa da shugaban kasar Indiya

"Ka tabbata da ace mahaifinka na cikin wannan gwamnati za ka furta hakan?"

- Hadiza El-Rufai

Obasanjo ya caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa, Cif Olusegun Obasanjo ya caccaki tsarin da Bola Tinubu ke bi wajen gudanar da gwamnati.

Tsohon shugaban kasan ya yi zargin cewa Bola Ahmed Tinubu ba shi da wata sahihiyar hanya ta magance matsalolin da su ka damu Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng