An Dawo da Kwamishinan Jigawa Aiki bayan Zargin Zina da Matar Aure
- Gwamnatin Jigawa ta dawo da kwamishinan ayyuka na musamman, Auwalu Danladi Sankara bakin aiki bayan an dakatar da shi
- Gwamna Umaru A. Namadi ya dakatar da kwamishinan ne yayin da hukumar Hisba ta jihar Kano ta zarge shi da zina da matar aure
- Sai dai bayan bincike, wata kotun shari'ar Musulunci a jihar Kano ta wanke Auwalu Danladi Sankara daga zargin da aka masa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar A. Namadi ya dawo da kwamishinan da aka dakatar saboda zargin zina.
Gwamna Umar Namadi ya dakatar da kwamishinan ne saboda a samu damar masa bincike yadda ya kamata.
Jami'in yada labaran gwamnatin Jigawa, Garba Muhammad ne ya sanar da dawo da Auwalu Danladi Sankara a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dawo da kwamishinan Jigawa aiki
Kwamishinan ayyuka na musamman a jihar Jigawa ya dawo bakin aiki bayan dakatar da shi da aka yi a baya.
Gwamna Umar Namadi ya dawo da kwamishinan ne bayan kotun Musulunci ta wanke shi daga zargin zina da aka masa.
An ruwaito cewa sakataren gwamnatin Jigawa, Bala Ibrahim ne ya mika takardar dawowa aiki ga kwamishinan.
"Idan za a iya tunawa, an dakatar da kwamishinan ne saboda wani zargi da aka masa a gaban hukumar Hisba ta jihar Kano.
Kuma an dawo da shi bakin aiki ne saboda wanke shi daga zargin da babbar kotun shari'ar Musulunci ta yi a Kano."
- Bala Ibrahim, Sakataren gwamnatin Jigawa
A yanzu haka dai Auwalu Danladi Sankara zai koma bakin aiki kamar yadda ya saba ba tare da wani jinkiri ba.
Jigawa: An gargadi masu ta da rikici a APC
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar A. Namadi ya dawo gida bayan shafe kwanaki 18 a kasar waje inda ya tarar da wani rikici a cikin jam'iyyar APC.
Mai girma Umar A. Namadi ya gargadi masu neman raba jam'iyyar gida biyu inda ya tabbatar da cewa APC za ta cigaba da zama daya a jihar Jigawa.
Asali: Legit.ng