An Fatattaki Jami'an EFCC daga Aiki bayan Kama Su da Rashawa Dumu Dumu

An Fatattaki Jami'an EFCC daga Aiki bayan Kama Su da Rashawa Dumu Dumu

  • Hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta fara shirin kawo gyara a ayyukan da take gudanarwa
  • Shugaban EFCC, Ola Olukoyede ya bayyana cewa hukumar ta dauki matakin korar wasu jami'ai saboda kama su da laifi da aka yi
  • Ola Olukoyede ya kara da cewa bayan korarsu, dole hukumar za ta dauki matakin ladabtar da su domin toshe kofar barna a gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar EFCC ta fatattaki wasu jami'ai saboda kaman su da laifin cin hanci da rashawa.

Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce bai kamata a samu jami'in EFCC da laifin cin hanci da rashawa ba.

Ola Olukoyede
An kori jami'an EFCC saboda rashawa. Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Ola Olukoyede ya yi bayani ne a wani taro a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

'Ko sai kowa ya mutu ne,' Dattawan Arewa sun yi raddi ga Tinubu kan tsadar rayuwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC ta kori jami'ai saboda rashawa

Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ya tabbatar da cewa hukumar ta kori wasu jami'anta guda biyu saboda rashawa.

Peopels Gazette ta wallafa cewa Ola Olukoyede ya ce hakan na cikin wasu tsare tsare da suke kawowa domin tsaftace aikinsu a Najeriya.

Shugaban ya kuma tabbatar da cewa dole hukumar za ta dauki matakin ladabtar da wadanda aka kora daga aiki daga yanzu.

Ana yin gyare-gyare a hukumar EFCC

"Muna kan wasu gyare-gyare a halin yanzu. A mako biyu da suka wuce mun kori wasu jami'ai biyu.
Ba yadda za a yi a ce ka na yaki da rashawa amma kuma a same ka da laifin da aka dauke ka aiki domin ka kawar da shi.
Za mu hukunta duk wanda muka kora kamar yadda suma suke hukunta masu laifin da suka kama."

- Ola Olukoyede, shugaban EFCC

Shugaban kara da cewa ya san akwai bata gari a cikin jami'an EFCC, saboda haka ya bukaci a sanar da shi da zarar an gano su domin daukar mataki.

Kara karanta wannan

An miƙawa gwamnatin Tinubu buƙatar daukar mataki kan haihuwa barkatai

A karshe, Ola Olukoyede ya bukaci dukkan wadanda suke da shawara a kan ayyukan hukumar su tuntube su.

Bobrisky ya kai karar hukumar EFCC

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen dan daudu, Bobrisky ya shigar da ƙarar EFCC da majalisar tarayya, yana zargin sun take haƙƙinsa ta hanyar tsare shi.

Dan daudun ya ce gayyatar da majalisar tarayya ta masa domin bincike samo asali ne daga wani sautin murya da ba a tabbatar da sahihancinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng