Gwamna Ya Sanar da Sabon Albashin da Zai Fara Biyan Ma'aikata, Ya Yi Ƙarin Fansho

Gwamna Ya Sanar da Sabon Albashin da Zai Fara Biyan Ma'aikata, Ya Yi Ƙarin Fansho

  • Gwamna Biodun Oyebanji ya amince da N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan gwamnati a jihar Ekiti
  • A wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Mai girma Gwamna Oyebanji ya ce ƙarin albashin zai shafi har ƴan fansho da ke jihar
  • Mai taimakawa gwamnan na musamman kan harkokin sadarwa, Tanimola Kolade ya tabbatar da labarin a wata sanarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Gwamna Biodun Oyebanji na Ekiti ya amince zai fara biyan ma'aikata N70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan ya kuma tabbatarwa ma'aikata cewa babu wanda za a bari a baya, dukkansu a kowane mataki za su fara karɓar sabon albashi a tare.

Gwamma Oyebanji da ƴan kwadago.
Gwamnan Ekiti ya amince zai fara biyan sabon mafi karancin albashi na N70,000 Hoto: Biodun Oyebanji, Nigeria Labour Congress
Asali: Facebook

Gwamna ya yi ƙarin albashi a jihar Ekiti

Mai taimakawa gwamnan kan harkokin sadarwa, Tanimola Kolade ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin X ranar Talata.

Kara karanta wannan

Gwamna ya yi ƙarin albashi, ya ɗara yadda Tinubu ke biyan ma'aikata

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce bayan ma'aikata, gwamnan ya amince da yi wa ƴan fansho ƙarin albashin da ake ba su duk wata.

Idan ba ku manta ba ƙungiyar kwadago NLC ta umarci rassanta na jihohi da su fara yajin aiki ranar 1 ga Disamba, idan gwamnoni ba su fara biyan sabon albashi ba.

Gwamna Oyebanji ya amince da N70,000

Mista Kolade ya wallafa a shafinsa cewa:

"Gwamnatin jihar Ekiti ta amince da N70,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma'aikata kuma ta amince da dukkan tsare-tsaren aiwatarwa.
"Sabon albashin zai shafi kowane ɓangare na ma'aikata har ma da ƴan fansho.
Gwamna Oyebanji ya cika alƙawarin da ya ɗauka cewa ba wanda za a bari a baya."

Wannan dai na zuwa ne kimanin wata ɗaya bayan Gwamnan Ekiti ya bai wa wasu ma'aikata kyautar Naira miliyan 42 bisa namijin ƙokarin a suka yi.

Gwamna Alia zai fara biyan N75,000

Kara karanta wannan

Badaƙalar N1.3trn: Tsohon gwamna ya faɗi waɗanda suka turo masa EFCC

A wani rahoton, an ji cewa gwamnatin Benue ta sanar da ƙarin albashin ma'aikata zuwa N75,000 bayan wani zama da ta yi da kungiyar kwadago.

Gwamna Hyacinth Aliya ya bayyana dalilin zarce N70,000 da gwamnatin tarayya ta ayyana a matsayin mafi ƙarancin albashi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262