Gwamna Ya Cire Tsoro, Ya Bayyana Wasu 'Ƴan Siyasa' da Ke Ɗaukar Nauyin Ƴan Bindiga
- Gwamna Alex Otti ya yi ikirarin cewa gwamnatinsa ta gano wasu ƴan siyasa da ke ɗaukar nauyin hare-haren ƴan bindiga a Abia
- Otti ya ce bayanan da aka tattara daga nutane da wasu majiyoyi sun nuna babu hannun ƙungiyar ƴan aware IPOB a matsalar tsaron jihar
- Ya ce gwamnatinsa ba za ta ɗaga wa kowa kafa ba, za ta sa kafar wando ɗaya da duk mai hannu a hare-haren ƴan bindiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na Abia ya ce 'yan siyasa na tsagin adawa tare da wasu 'baƙi' ne suke rura wutar matsalar tsaro da ayyukan ta'addanci a jihar.
A ƴan kwanakin nan matsalar tsaro ta ƙara taɓarɓarewa a jihar Abia, inda ƴan bindiga ke kara zafafa kai hare-hare kan jami'an tsaro da sauran al'umma.
Gwamnatin Najeriya ta sha zargin kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra (IPOB) da hannu wajen kai munanan hare-hare a Kudu maso Gabas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otti ya fallasa masu ɗaukar nauyi
Amma da yake martani, Gwamna Otti ya ce gwamnatinsa ta gudanar da bincike mai zurfi kuma ta gano masu ɗaukar nauyin kai hare-hare, Premium Times ta ruwaito.
Alex Otti ya ce bayanai sun nuna babu ruwan IPOB a hare-hare da ake kai wa, wasu ƴan adawar siyasa ne ke ɗaukar nauyin ƴan bindigar da suka addabi jama'a.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Abia, Ferdinand Ekeoma ya fitar ranar Litinin.
Wane ƴan siyasa gwamnan ke zargi?
Gwamnan ya ce ‘yan siyasar da ake zargin da har yanzu ba a faɗi sunayensu ba sun fara daukar nauyin tashe-tashen hankula ne a karshen watan Mayun bana.
A rahoton Vanguard, Otti ya ce:
"Burinsu kawai ka da a zauna lafiya saboda ta hakan kaɗai za su ɗauke hankalin gwamnati daga yin ayyukan da za su kawo ci gaban Abia."
Gwamna Otti ya ce babu sassauci
Otti ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta sassauta wa duk wanda ta kama da hannu a matsalar tsaro ba, za ta zaƙulo su kuma ta fatattake su daga Abia.
Ya ce gwamnatinsa za ta sa kafar wando ɗaya da duk wani mai ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiya da kwanciyar hankali mutanen Abia.
Gwamnan Abia ya yi tir da kisan sojoji
Kun ji cewa gwamnan Abia, Alex Otti ya nuna takaicinsa kan ɗanyen aikin da ƴan bindiga suka aikata na kashe sojoji a jiharsa.
Alex Otti ya nuna alhininsa kan kisan tare da jajantawa rundunar sojojin Najeriya kan rashin jami'an tsaron da aka yi a Kudu maso Gabashin Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng