'Yadda Bola Tinubu Ke Aiki Tukuru domin Ceto Yan Najeriya daga Kangin Talauci
- Wale Edun ya bayyana irin kokarin da shugaban ƙasa, Bola Tinubu ke yi don ceto ƴan Najeriya daga kangin talauci
- Ministan kudin ya ce Bola Tinubu ya damu da halin da mutane ke ciki kuma yana iya kokarinsu wajen shawo kan lamarin
- Edun ya ce gwamnatin Tinubu ta gaji tarin matsaloli daga gwamnatin da ta shuɗe amma ba za ta tsaya ɓata lokaci a kansu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ministan Kudi da harkokin tattalin arziki, Wale Edun, ya ce shugaban kasa Bola Tinubu na tsara hanyar fitar da dimbin ‘yan Najeriya daga kangin talauci.
Edun ya bayyana haka ne ranar Litinin a Bauchi a wurin bude taron majalisar kudi da tattalin arziki ta ƙasa (NACOFED) na bana 2024.
Ministan ya ce Shugaba Tinubu na aiki ba dare ba rana domin ƴan Najeriya su samu sauƙin rayuwa ta hanyar kawo tsare-tsaren da kowa zai amfana, Daily Trust ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bola Tinubu na kokarin yaye talauci
A cewarsa, gwamnatin Tinubu ta gaji tarin matsaloli daga gwamnatin da ta gabata amma ba ta tsaya ɓata lokaci ba ta fara nemo hanyoyin magance su.
"Shugaban kasa na kokarin jawo mau zuba jari a gida da ƙasashen ketare dokin bunkasa tattalin arziki, samar da ayyuka. yi da ceto mutane daga kangin talauci.
"Ya toshe ƙofar da ake kwashe kaso biyar na tattalin arziki duk shekara, ya cire tallafin mai da na Naira wanda wasu tsiraru kaɗai ke amfana da shi."
"Wasu yan ƙalilan ne ke cin moriyar waɗannan kuɗaɗe da akw warewa amma sauran ƴan Najeriya ba su amfana da komai."
- Wale Edun.
Ƴan Najeriya za su amfana da kudin tallafi
Ministan ya ce dakatar da biyan waɗannan kudi ya kara yawan kuɗaɗen shiga wanda kai tsaye ke kasafta su zuwa jihohi da kananan hukumomi.
Edun ya kuma ƙara da cewa gwamnatoci a kowane mataki na da damar amfani da waɗannan kuɗi wajen gina al'umma, Vanguard ta ruwaito.
Bola Tinubu zai ƙara karɓo rancen kudi
A wani rahoton, kun ji cewa majalisar zartarwa ta tarayya ta amince da shirin karbo rance na Naira tiriliyan 4.199 domin tallafa wa tattalin arzikin Najeriya.
Ministan tattali, Wale Edun, ya bayyana cewa za a yi amfani da kudin wajen inganta tattalin arzikin ta hanyar manyan ayyuka.
Asali: Legit.ng