Sankara: Kotu Ta Yi Hukunci kan Kwamishinan da Ake Zargi da Lalata da Matar Aure
- Kotun shari'ar Musulunci da ke jihar Kano ta yi hukunci kan ƙarar da aka shigar da kwamishinan ayyuka na musamman a Jigawa
- Alƙalin kotun ya wanke Auwal Danladi Sankara daga zargin da ake yi masa na yin lalata da matar aure, tuhumar da ya karyata tuni
- Kotun ta zartar da wannan hukuncin ne bayan ta samu rahoton binciken da ƴan sanda suka gudanar kan zargin da ake yi wa kwamishinan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano, ta yi hukunci kan ƙarar da aka shigar da kwamishinan ayyuka na musamman na Jigawa, Auwal Danladi Sankara, bisa zargin lalata da matar aure.
Kotun ƙarƙashin jagorancin mai shari'a, Ibrahim Sarki Yola ta wanke kwamishinan daga zargin yin lalata da wata matar aure.
Kotu ta wanke kwamishinan Jigawa daga lalata
Tashar Channels tv ta rahoto cewa alƙalin kotun ya yanke wannan hukuncin ne bayan ya samu rahoton binciken da ƴan sanda suka gudanar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nasiru Buba ne ya shigar da ƙarar, inda ya zargi Sankara da yin lalata da matarsa, Tasleem Baba Nabegu.
Da yake yanke hukuncin, Ibrahim Sarki Yola ya jaddada buƙatar jami’an tsaro da hukumomi irin su Hisbah su riƙa gudanar da bincike na tsafta.
Ya yi nuni da cewa dole ne a yi taka tsan-tsan kan zarge-zargen da ake yi wa fitattun mutane domin kaucewa ɓata suna ba gaira ba dalili, rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar.
"Bayan binciken da ofishin mataimakin babban sufeton ƴan sanda ya gudanar, rahoton ya nuna babu wata shaida da ke tabbatar da cewa akwai wata alaƙa mara kyau a tsakanin Auwal Danladi Sankara da Tasleem Baba Nabegu."
"Tun da wanda ya shigar da ƙarar da lauyoyinsa ba sa nan domin ƙalubalantar binciken da ƴan sanda suka gabatar, ba ni da wani zaɓi illa na soke ƙarar."
- Ibrahim Sarki Yola.
Me waɗanda ake ƙara suka ce?
Da yake magana a madadin Sankara, lauyansa, Barista Sadam Suleiman, ya bayyana jin daɗinsa kan hukuncin.
"Kodayaushe muna faɗin cewa wanda muke karewa ba shi da laifi. Kotun ta tabbatar da hakan ta hanyar wanke sunansa bisa binciken da ƴan sanda suka gudanar."
- Sadam Suleiman
A halin da ake ciki, lauyan Tasleem Baba Nabegu, Rabiu Shu’aibu, ya nuna cewa akwai yuwuwar ɗaukar matakin shari’a kan Nasiru Buba bisa zargin ɓata sunan wacce yake karewa.
"Za mu tattauna da wacce muke karewa domin duba yiwuwar shigar da ƙara kan Nasiru Buba, saboda ya ɓata sunanta."
- Rabiu Shu'aibu.
Hisbah ta canza magana kan kwamishinan Jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah a Kano ta yi amai ta lashe kan zargin kwamishina a jihar Jigawa, Auwal Danladi Sankara.
Jami'in hukumar ya janye zargin da ake yi wa kwamishinan ayyuka na musamman da yin lalata da wata matar aure.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng