Fadar Shugaban Ƙasa Ta yi Martani Mai Zafi ga Obasanjo, Ta Tono 'Kurakuransa'
- Fadar shugaban kasa ta yi martani ga tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan sukar Bola Ahmed Tinubu da ya yi
- Sabonadimin shugaba Bola Tinubu, Sunday Dare ne ya ce Obasanjo ba shi da hurumin sukar wata gwamnati a Najeriya
- Dare ya kara da cewa a lokacin Olusegun Obasanjo an gurgunta dimokuraɗiyya wanda har yanzu ba a kammala gyara ta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Bayan sukar Bola Tinubu da Olusegun Obasanjo ya yi, fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi.
Hadimin shugaban kasa a harkokin sadarwa, Sunday Dare ya ce mulkin Obasanjo ne ya jefa Najeriya cikin tarin matsalolin da ake fama da su.
Legit ta tatttaro bayanai kan maratanin da Sunday Dare ya yi ga Obasanjo ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Olusegun Obasanjo bai kyauta ba inji Dare
Hadimin shugaban kasa, Sunday Dare ya ce abin da Obasanjo ya fada a jami'ar Yale a Amurka a kan gazawar Tinubu ba gaskiya a ciki.
Punch ta wallafa cewa Sunday Dare ya ce kowa ya san Obasanjo da cakuɗa alkaluma kuma yan Najeriya ba za su dauki maganarsa ba.
Maganar lantarki a lokacin Obasanjo
Sunday Dare ya ce a lokacin gwamnatin Obasanjo an samu cin hanci sosai amma kuma wai yau shi ne mai magana a kan rashawa.
Dare ya yi zargin cewa an rasa kudin gyaran wutar lantarki $16bn a lokacin Obasanjo wanda har yau ba a samu labarin kudin ba.
Dimokuraɗiyya a lokacin Obasanjo
Hadimin shugaban kasar ya ce a lokacin mulkin Obasanjo aka gurgunta dimokuraɗiyya a Najeriya saboda neman mulki karo na uku.
Sunday Dare ya ce tun da Obasanjo ya gama mulki ake ƙoƙarin share dattin da ya kawo Najeriya wanda yanzu haka aikin da Tinubu ke yi kenan.
A karshe, Dare ya kara da cewa babu abin da zai kawar da hankalin Bola Tinubu daga ayyukan cigaba a Najeriya a halin yanzu.
Kudirin Tinubu ya kara samun baranza
A wani rahoton, kun ji cewa sabani tsakanin gwamnoni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan kudirin haraji na kara girma, an fara yi wa yan majalisa barazana.
Mataimakin shugaban yada labaran majalisar wakilai ya bayyana cewa yan majalisa sun fara fuskantar barazana daga gwamnonin jihohinsu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng