IPMAN da Dangote Sun Kulla Yarjejeniyar Samar da Fetur Lita Miliyan 240 duk Wata
- Matatar Dangote da kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) sun cimma matsaya kan samawa 'yan Najeriya fetur
- A duk mako, matatar Dangote za ta rika ba yan kasuwar IPMAN lita miliyan 60 na fetur, wanda ke nufin lita miliyan 240 a wata
- Wannan na zuwa bayan kungiyar IPMAN ta tabbatar da cewa za a samu saukin farashin fetur da zarar ta fara dauko man Dangote
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos - Bayan cimma matsaya tsakanin kungiyar dillalan man fetur na kasa (IPMAN) da matatar man fetur ta Dangote, an cimma yarjejeniyar samar da mai ga yan kasa.
Matatar Dangote ta yi wa yan kasuwar tayin sama mata litar fetur miliyan 60 a duk mako domin wadata yan kasar nan.
Jaridar Punch ta ruwaito cewa wannan na nufin matatar za ta rika sayarwa yan kasuwar IPMAN tataccen fetur lita miliyan 240 duk wata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
IPMAN: Yadda Dangote zai samar da fetur
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa matatar Dangote da ke Legas na shirin fara sayo danyen mai daga kasashen waje domin samar da tataccen fetur.
Wannan na zuwa bayan ta sanya hannu a kan yarjejeniyar da ake sa ran wadata yan kasuwar fetur domin yan Najeriya.
IPMAN za ta dauko fetur daga matatar Dangote
Sakataren yada labarai na kungiyar IPMAN na kasa, Chinedu Ukadike ya bayyana cewa sun shirya dakon fetur daga matatar Dangote.
“Za mu rika dauko fetur miliyan 60 duk mako. Kuma za mu iya raba shi ga sassan kasar nan da zarar mun fara dakon fetur din daga matatar," cewar Chinedu Ukadike.
"Farashin fetur zai karye:" cewar IPMAN
A baya mun ruwaito cewa kungiyar dillalan man fetur ta kasa (IPMAN) ta bayyana cewa za a samu saukin farashin litar fetur a kasar nan da zarar an fara jigilar mai daga Dangote.
Shugaban IPMAN, Abubakar Garima da ya bayyana haka ya kara da cewa tuni aka fara warware sabanin da ke tsakanin kungiyar da matatar Dangote, kuma za a fara dakon fetur kai tsaye.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng