Kwana Ya Kware: Tsohon Shugaban Hukumar NIA Ya Rasu Yana da Shekara 81
- An yi babban rashi a jihar Katsina bayan rasuwar tsohon shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA)
- Ambassada Ibrahim Zakari ya yi bankwana da duniya ne yana da shekara 81 a duniya a ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamban 2024
- Gwamna Dikko Umaru Radda ya nuna alhininsa kan rasuwar marigayin wanda yake riƙe da sarautar Talban Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Tsohon Darakta-Janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA), Ambasada Zakari Ibrahim, ya rasu.
Marigayin ya yi bankwana da duniya ne yana da shekaru 81.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Ambasada Zakari Ibrahim ya rasu ne da sanyin safiyar ranar Lahadi, 17 ga watan Nuwamban 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane ne Ambassada Ibrahim Zakari?
Ambasada Ibrahim, wanda ɗan jihar Katsina ne, yana riƙe da sarautar gargajiya ta Talban Katsina, a cikin masarautar Katsina.
Ya kasance abokin karatun tsohon shugaban Najeriya, Muhammad Buhari a kwalejin gwamnatin Katsina (GCK).
Talban Katsina ya taɓa riƙe muƙamin Darakta-Janar na hukumar leƙen asiri ta ƙasa (NIA) daga 1993 zuwa 1998.
Ya kuma riƙe muƙamin ƙaramin ministan harkokin waje a farkon shekarun 1990. A shekarar 2011, shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya naɗa Talban Katsina domin jagorantar ayyukan yaƙi da ta'addanci na ƙasa.
A cewar wata majiyar, ana sa ran gawar Ambasada Zakari Ibrahim, za ta isa jiharsa ta Katsina a yammacin Lahadi domin binne shi.
Gwamna Radda ya yi ta'aziyya
Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda ya bayyana matuƙar baƙin cikinsa dangane da rasuwar Ambasada Zakari Ibrahim.
A wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaransa, Kaula Mohamed ya fitar, Gwamna Radda ya bayyana marigayi Ambasada Ibrahim a matsayin haziƙin ɗan Katsina wanda ya hidimtawa Najeriya a muƙamai daban-daban.
Shugaban ƙaramar hukuma ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa an shiga ruɗani a jihar Legas bayan mutuwar bazata da shugaban karamar hukuma ya yi cikin wani irin yanayi.
Hakan ya faru ne bayan rasuwar shugaban karamar hukumar Onigbongbo, Oladotun Olakanle a ranar Asabar 2 ga watan Nuwambar 2024.
Asali: Legit.ng