Shugaba Tinubu Ya Karrama Firaministan India da Lambar Yabo ta Kasa, Bidiyo Ya Bayyana

Shugaba Tinubu Ya Karrama Firaministan India da Lambar Yabo ta Kasa, Bidiyo Ya Bayyana

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙarbi baƙuncin firaministan India, Narendra Modi a fadarsa da ta Aso Rock Villa da ke Abuja
  • Tinubu ya karrama Narendra Modi da lambar yabo ta ƙasa ta GCON wacce ita ce mafi girma ta biyu a Najeriya
  • Shugabannin biyu dai za su tattauna domin ƙara ƙarfafa kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Najeriya da India inda ake sa ran za su rattaɓa hannu kan yarjeniyoyi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya karrama firaministan India, Narendra Modi, bayan ya kawo ziyara a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya ba Narendra Modi lambar yabo mafi girma ta biyu a Najeriya, ta GCON.

Tinubu ya karrama Narendra Modi
Shugaba Tinubu ya ba Narendra Modi lambar yabo Hoto: @NgNewsAgency
Asali: Twitter

Hadimin Shugaba Tinubu kan kafafen sada zumunta Dada Olusegun ne ya bayyana hakan a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya karrama Narendra Modi

Kara karanta wannan

Lagbaja: A ƙarshe, an birne gawar marigayi tsohon hafsan sojoji a Abuja

Shugaba Tinubu ya karrama Narendra Modi ne a wata ganawa da suka yi a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock Villa, Abuja.

Shugaban ƙasan ya bayyana cewa an karrama Narendra Modi ne domin nuna godiya ga India a matsayin abokiyar Najeriya.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karrama firaminista Narendra Modi. Ya ba shi lambar yabo mafi girma ta biyu a Najeriya ta Grand Commander of the Order of Niger (GCON). Ya bayyana shi a matsayin abokin Najeriya.

- Dada Olusegun

Narendra Modi ya samu tarba a Villa

Narendra Modi, wanda ya isa Abuja da yammacin ranar Asabar, an tarbe shi ne a bakin kofar fadar Villa da misalin ƙarfe 10:20 na safiyar ranar Lahadi.

Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna tare da rattaba hannu kan yarjeniyoyi da dama a ganawarsu ta sirri.

A cewar fadar shugaban ƙasa, Tinubu da Narendra Modi za su nemi ƙara ƙarfafa alaƙar Najeriya da India a wannan ziyarar.

Kara karanta wannan

Lagbaja: Shugaba Tinubu ya karrama marigayi hafsan sojojin ƙasa a wurin jana'iza

Tinubu ya karrama Lagbaja

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Ahmed Tinubu ya halarci jana'izar marigayi hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Shugaba Tinubu ya karrama marigayi shugaban sojojin da lambar yabon CFR ta ƙasa a wurin jana'izarsa a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng