Bayan Birne Lagbaja, CDS Ya Tura Muhimmin Sako ga Sojojin Najeriya
- Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Christopher Musa, ya nuna alhininsa kan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Abiodun Lagbaja
- Christopher Musa ya buƙaci sojojin Najeriya da su ƙara.jajircewa wajen fatattakar maƙiyan ƙasar nan domin karrama tsohon babban hafsan sojojin ƙasa (COAS)
- An yi jana'ozar marigayin ne dai a ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamban 2024 a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke babban birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Babban hafsan hafsoshin tsaron Najeriya (CDS), Christopher Musa, ya tura saƙo ga sojoji kan rasuwar Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Christopher Musa ya ce ya kamata sojojin Najeriya su sake sadaukar da kansu wajen fatattakar maƙiyan ƙasar nan domin karrama Taoreed Lagbaja, tsohon babban hafsan sojoji (COAS).
Christopher Musa ya yi wannan jawabi ne a ranar Juma’a a maƙabartar sojoji ta ƙasa yayin jana’izar Lagbaja, cewar rahoton jaridar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me CDS ya gayawa sojoji kan rasuwar Lagbaja?
Babban hafsan hafsoshin ya kuma buƙaci sojoji da su yi amfani da mutuwarsa wajen ƙara jajircewa domin cimma manufofin da ya tsaya a kai.
Taoreed Lagbaja ya mutu ne yana da shekara 56 a duniya bayan ya yi fama da wata cuta da ba a bayyana ba.
"Mu tabbatar cewa sadaukarwarsa da hidimarsa sun ci gaba da jagorantar matakanmu yayin da muke kare wannan ƙasa mai girma."
"Za mu yi amfani da mutuwarsa domin mu ƙara azama wajen fatattakar duk maƙiyan ƙasar nan a duk inda suke, a ciki ko waje."
- Christopher Musa
Ya bayyana marigayi Lagbaja a matsayin mutum mai kula da iyalansa, abin koyi kuma aboki, wanda za a ji raɗaɗin rashinsa.
Tinubu ya karrama Lagbaja
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Ahmed Tinubu ya halarci jana'izar marigayi hafsan rundunar sojojin ƙasa ta Najeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.
Shugaba Tinubu ya karrama marigayi shugaban sojojin da lambar yabon CFR ta ƙasa a wurin jana'izarsa ranar Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2023.
Asali: Legit.ng