Wutar Lantarki: Gwamna Ya Fusata, Ya Kori Shugaban Kamfanin IPCL Nan Take
- Gwamna Umo Eno na Akwa Ibom ya kori shugaban kamfanin wutar lantarki na jihar (IPCL), Injiniya Meyen Etukudoh
- An ruwaito cewa matakin gwamnan ba zai rasa alaƙa da ɗaukewar wutar lantarki na kusan kwanaki uku a jihar Kudun
- Eno ya umarci shugaban kamfanin ya miƙa dukkan abubuwan da ke hannunsa ga kwamishinan makamashi nan take
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, ya kori Manajan Darakta (MD) na kamfanin lantarki na jihar (IPCL), Engr. Meyen Etukudoh.
Gwamna Eno ya sallami shugaban kamfanin IPCL daga aiki kuma ya ce matakin zai fara aiki ne nan take daga yau Juma'a, 15 ga watan Nuwamba, 2024.
Dalilin Gwamna Eno na korar shugaban IPCL
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa kusan kwanaki uku kenan babu wutar lantarki a jihar Akwa Ibom da ke Kudancin Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakan ya sa ake tunanin Gwamna Umo Edo ya kori shugaban kamfanin IPCL saboda ɗaukewar wuta na tsawon kwanaki a faɗin jihar.
Ɗaukewar wutar ya janyo wa ‘yan kasuwa asara tare da jefa mazauna Akwa Ibom cikin wahalhalu duk da miliyoyin da gwamnatin jihar ta zuba a harkar lantarki.
Gwamna Eno ya umurci Etukudoh da ya mika dukkan kayan kamfanin da takardun da ke hannunsa ga kwamishinan makamashi.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwar da sakataren gwamnatin jihar, Prince Enobong Uwah ya fitar.
Gwamna Eno ya damu da ɗaukewar wuta
Jami'in ya ce gwamnan ya damu da yadda Etukudoh ya kasa amfani hazakarsa wajen sake fasali da gyara ɓangaren lantarki daidai da kudirin gwamnatin jihar.
"A wani ɓangare na garambawul a gwamnatinsa, mai girma gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya sallami shugaban kamfanin wuta, Engr. Meyen Etukudoh nan take."
"Bisa haka an umurci Etukudoh da ya mika harkokin gudanar da kamfanin ga kwamishinan makamashi," in ji sanarwar.
TCN ya fara gyaran wuta a Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya sanar da dawo da wutar lantarki a layin wutar Ugwuaji-Apir mai ƙarfin 330kV.
A ranar 22 ga Oktoba, TCN ta bayar da rahoton rashin wuta a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma, sakamakon matsala a layukan lantarki biyu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng