Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Karar da Wasu Gwamnoni Suka Nemi a Rusa EFCC

Kotun Ƙoli Ta Yanke Hukunci kan Karar da Wasu Gwamnoni Suka Nemi a Rusa EFCC

  • Kotun koli ta raba gardama kan takaddamar da ake ta yi kan halascin dokar da ta kafa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa watau EFCC
  • Tun farko wasu jihohi sun tunkari kotun, iɓda suka nemi ta rusa hukumar gaba ɗaya saboda ta saɓawa kundij tsarin mulkin Najeriya
  • Jihohin da suka shigar da wannan kara sun haɗa da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nassarawa, Kebbi, Katsina, Sokoto, Jigawa, da Enugu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Kotun kolin Najeriya ta yi fatali da karar da wasu jihohi suka shigar gabanta suna kalubalantar halascin kafa hukumar EFCC.

A farko dai Antoni Janar kuma kwamishinonin shari'a na jihohi 16 ne suka shigar da karar, inda suka bukaci kotun ta rushe hukumar EFCC.

Kotun koli.
Kotun koli ta yi watsi da karar da aka nemi rusa hukumar EFCC Hoto: Supreme Court
Asali: Twitter

Sai dai bayan fara shari'ar, wasu jihohi daga ciki sun janye yayin da wasu kuma suka shiga domin tama takwarorinsu wannan faɗa, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Babban alƙalin jihar Yobe zai dawo da albashin shekaru 12, an dakatar wasu 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC: Jihohin da suka kai kara kotun ƙoli

Jihohin da suka shigar da ƙarar a farko sun hada da Ondo, Edo, Oyo, Ogun, Nassarawa, Kebbi da kuma Katsina.

A cikin jihohin akwai Sokoto, Jigawa, Enugu, Benuwe, Anambra, Filato, Kuros Riba da Neja.

Da aka fara zaman shari'ar ranar 22 ga watan Oktoba, jihohin Imo, Bauchi da Osun suka nemi a saka su a ciki yayin da Adamawa, Ebonyi da Anambara suka janye.

A bayanan jihohin da suka shigar da kara, sun shaidawa kotu cewa kundin tsarin mulki shi ne doka lamba ɗaya, don haka duk wani abu da ya saɓa masa haramun ne.

Dalilin shigar da ƙarar rushe hukumar EFCC

A cewarsu, dole sai mafi akasarin majalisun dokokin jihohi su amince sannan a kafa EFCC a bisa tanadin kundin tsarin mulki, amma ba a yi haka ba lokacin kafa hukumar.

Jihohin sun ƙara da cewa bai kamata dokar kafa EFCC ta yi aiki a jihohin da ba su amince da ita ba, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Lagbaja: A ƙarshe, an birne gawar marigayi tsohon hafsan sojoji a Abuja

A halin yanzu kotun ƙolin Najeriya ta yi fatali da dukkan korafe-korafen da jihohin suka shigar suna kalubalantar dokar kafa hukumar EFCC.

EFCC ta hana Okowa fita Najeriya

A wani rahoton, an ji cewa Hukumar EFCC ta karɓe fasfon tsohon gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa gabanin ta amince da bada belinsa.

Jami'an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa sun cafke Okowa ne bisa zargin karkatar da kudi da yake mulkin Delta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262